*_YAWAITA SADAKA GA MAI AZUMI_*

410 9 0
                                    

*_YAWAITA SADAKA GA MAI AZUMI_*

Manzon Allah s.a.w yakasance mai alkhairi mafi kyautar mutane,kuma yana kara zama mafi kyauta acikin watan Ramadhana lokacin da Mala'ika Jibirilu yake zauwa yana masa darasin Alquarani,kyautarsa da alkhairinsa yana karuwa sosai a wanann wata na Ramadhana fiye da kowane lokac.

*Mafi tsada da falalar sadaka itace wadda akayi a watan Ramadhana.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Mafi alkhairi sadaka,itace sadaka a cikin watan Ramadhana)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻋﻦ ﺃﻧﺲ.

*Daga cikin nau'in sadakar da ake so mutum ya yawaita a cikin watan Ramadhana*

Sadaka acikin watan Ramadhana tana da karin lada fiye da wani watan wanda ba Ramadhana ba,saboda aiyuka a watan Ramadhana a na rubunya ladarsa.

*A-Ciyar da Abinci*
Ciyar da abinci yana da cikin mafi girman aiyukan dha'a masu janyowa mutum albarka.

Allah yana cewa:
*‏(ﻭﻳﻄﻌﻤﻮﻥ ﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺣﺒﻪ ﻣﺴﻜﻴﻨﺎً ﻭﻳﺘﻴﻤﺎً ﻭﺃﺳﻴﺮﺍً.ﺇﻧﻤﺎ ﻧﻄﻌﻤﻜﻢ ﻟﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻧﺮﻳﺪ ﻣﻨﻜﻢ ﺟﺰﺍﺀً ﻭﻻ ﺷﻜﻮﺭﺍً ﺇﻧﺎ ﻧﺨﺎﻑ ﻣﻦ ﺭﺑﻨﺎ ﻳﻮﻣﺎً ﻋﺒﻮﺳﺎً ﻗﻤﻄﺮﻳﺮﺍً ﻓﻮﻗﺎﻫﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺷﺮ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﻭﻟﻘﺎﻫﻢ ﻧﻀﺮﺓً ﻭﺳﺮﻭﺭﺍً ﻭﺟﺰﺍﻫﻢ ﺑﻤﺎ ﺻﺒﺮﻭﺍ ﺟﻨﺔً ﻭﺣﺮﻳﺮﺍً)*
@ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ 8 ـ 12.

Hakika magabata na kwarai suna kokari da gaggauwa wajan ciyar da abinci ga mabuqata musamman a watan Ramadhana,domin samu ladar da Manzon Allah s.a w yake bada labari ga wanda yake ciyar da abincin ga mabuqata.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Ya ku masu imani ku ciyar da abinci ga ma'abuta buqata,sai Allah ya ciyar da ku daga 'yayan itatuwan aljanna,kuma wanda ya shayar da mai imani daga qishi,shi ma Allah zai shayar da shi daga Abin sha na gidan aljanna)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﺑﺴﻨﺪ ﺣﺴﻦ.

Wani daga cikin magabata yana cewa:
*"Na gaiyace abokaina mutum goma na ciyar da su abinci,yafi soyuwa a wajena akan na yanta wuyaye guda goma"*

Magabata daga cikin Sahabbai da Tabi'ai da Tabin'tabi'ai sun kasance basu yin bude baki sai tare da masu buqata da masu karamin karfi dan dacewa da lada mai yawa.

Abdillahi bin Mubarak ya kasance yana tanada abinci domin yin bude baki ga miskinai yana tarasu yana yi masu hidima dan neman aljanna awajan Allah.

Allah yana cewa:
‏(ﻟﻦ ﺗﺪﺧﻠﻮﺍ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﺣﺘﻰ ﺗﺆﻣﻨﻮﺍ ﻭﻟﻦ ﺗﺆﻣﻨﻮﺍ ﺣﺘﻰ ﺗﺤﺎﺑﻮﺍ)

*B-Ciyar da mai Azumi lokacin bude baki*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Wanda ya ciyar da mai Azumi lokacin bude baki,yana da ladan azumin dukkan wanda ya ciyar,ba tare da an rage masa wani abu ba)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ

A wani Hadisin Na Salman R.A Manzon Allah yana cewa:
*(Dukkan wanda ya ciyar da mai Azumi lokacin bude bakinsa,An gafarta masa zunubansa kuma an yan tashi daga shiga wuta,kuma yana da ladan azumin dukkan wanda ya ciyar,ba tare da an rage masa wani abu ba)*sai suka ce ya Manzon Allah?? Idan babu da abinci ciyar da su ba? Sai yace:
*(Ku ciyar da su ko da ruwane mai kyau ko dabino.....)*
@الترغيب والترهيب.

          
      Allah ne mafi sani.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now