*SHIN ASKE SUMAR JARIRI WAJIBI NE

330 0 0
                                    

*216 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN ASKE SUMAR JARIRI WAJIBI NE?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum, malam miye cikakken bayani a kan askin suna ga jarirai, shin wajibi ne ko kuma mutum na iya kyale yaronsa ba tare da an yi askin suna ba?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, jumhurun malaman Malikiyya da Shafi'iyya da Hanábila sun tafi kan cewa mustahabbi ne a aske gashin kan jariri a rana ta bakwai da haihuwarsa.

Sannan a yi sadaka da qimar nauyin gashin kansa da zinare ko azurfa a wurin Malikiyya da Shafi'iyya. Su kuma Hanábila a wurinsu da azurfa za a yi.  Idan kuma ba a yi masa askin ba, to za a yi kirdado sai a yi sadaka da gwargwadon nauyin gashin. Askin ya zamto bayan an yanka masa aqiqa ne.

Su kuma maz'habar Hanafiyya sun tafi a kan cewa aske gashin kan jariri halas ne, ba Sunnah ba ce, ba kuma wajiba ba ce, su suna ganin halasci ne kawai ba sunnanci ko wajabci ba, kawai a matsayin halas suke kallonsa.

Don ganin waɗannan bayanai a duba Almausú'atul Fiqhiyya Alkuwaitiyya (26/107).

Ibn Uthaimeen daga cikin malamai na wannan zamani ya ce: "Aske gashin kan yaro a rana ta bakwai da haihuwarsa Sunnah ce, hadisi ya zo da hakan daga Annabi ﷺ. Da sharaɗin mai askin ya zama qwararre ne da ba zai ji wa kan yaron rauni ba, ya zamo askin ba zai cutar da kan yaron ba, idan har haka ba zai yiwu ba, to ni ina ganin kada a yi askin nan, sai a yi sadaka da qimar nauyin gashin yaron da azurfa".
Duba Liqá'ul Bábil Maftooh (12/14).

Saboda haka idan aka dubi maganganun malaman nan duka, za a ga duk suna nuna rashin wajabcin aske gashin kan yaro, sai dai suna nuna Sunnah ce ko Mustahabbi ne, amma ba maganar wajabci. Sai dai duk da haka inda za a aske gashin kan yaro a rana ta bakwai, to hakan ya fi zamowa daidai a kan barinsa, duk da zamowarsa ba wajibi ba ne, saboda askewar ya dace qarara da aikin Manzon Allah ﷺ a hadisai ingantattu.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
15/09/2019 M.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now