*186 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN DOLE NE SAI NA GAISHE DA MIJIN WATA A GIDAN DA MUKE HAYA?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu, malam don Allah ina da tambaya, muna zaune gidan haya ne da mai gidan, to ita ma tana da mijinta, sai mijina ya ce in daina gaishe da mijin matan, to malam ya halatta in daina gaishe shi ko kuwa? Magode Allah ya kara ma malam lafiya.
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu Wa Rahmatullah, ƴar uwa shi dai gaisuwa al'ada ce mai kyau, amma ba wajibi ba ne, matuqar an aminta daga fitinuwa, to ya halasta mace ta gaisa da ajnabiyyi a wurin da ya kyautatu a yi hakan, gaisuwa a nan ba ana nufin musafaha ba ne, a'a, ana nufin gaisuwa irin ta al'ada 'Ina kwana ina wuni?' To amma mu yanzu ba mu san dalilin da ya sa mijin naki yake hana ki gaishe da mijin ƴar gidan naku ba, don haka sai ki nuna masa maslahar da ya sa kike gaishe shi, idan bai gamsu ba, to shi kenan sai ki daina ɗin, saboda kada qin dainawarki ya haifar da wata matsala a tsakaninku, tun da dai dama gaisuwar ba wajibi ba ne.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
19/11/1440 h.
22/07/2019 m.
![](https://img.wattpad.com/cover/186935965-288-k193559.jpg)
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: