*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN ALLAH YA ISAN MIJI ZAI BI MATA?*
TAMBAYA:
Assalamu Alaikum, Malam mijina wani irin mutum ne mai gadara da Isa, kuma mu uku ne a gunsa ga yara, idan ya ba da abinci sai ya ce ba ya son farin magi, kuma kudin ba ya isa, idan aka sa ka sai ya yi Allah ya isa, shin za ta bi mu ko kuwa? na gode.
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, Babu shakka a kan cewa duk wanda ya yi maka Allah ya isa za ta bi ka matuqar akwai wani haqqinsa a kanka da ya sa ya yi maka Allah ya isa saboda shi, ballantana kuma mijin mace, wanda girman haqqin miji a kan mace yakan qetare haqqin iyayenta a kanta idan ta yi aure, saboda haka kada ku sa magin da mijinku ba ya so a sa masa a abinci, hakan shi ne abin da yake dai-dai ko da kuɗin ba ya kaiwa, duk ranar da ya ji abincin bai yi masa ɗanɗano ba, sai ku yi masa bayani cikin natsuwa a kan kuɗin ne ba ya isa a iya siyan kayan girkin da ya fi so a yi amfani da su, ina ganin hakan zai fi zama maku dai-dai.
Idan kuma ba ku taɓa faɗa masa kuɗin ne ba ya kaiwa ya sa kuke sa masa farin magi ba, to sai ku sanar da shi dalilin da ya sa kuke son sa farin magi saboda kuɗin ne ba ya isa, in Allah ya so zai fahimce ku.Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
26/6/1440 h.
03/03/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: