Assalamu alaikum Allah mlm ina da tambaya ni yarkasuwace inaseida kaya Wanda ma bana sayarwa inkace kanaso nakansayo inkawo maka inkara riba wasukuma kudin sukebani insayo musu to nikuma inna sayo see inkara riba ya halatta inkara riban ?
*AMSA*
Idan mutum ya baka sautu ko kuma muce ya wakiltaka ka siyomasa wani abu, bai dace kayimasa Karin komai ba cikin kudin, sabida amanace aka baka, don haka idan asami ragima zaka mayar masa da canjinsa, sai dai idan shi ya dauka ya bayar.
Amma ya halatta a nemi ladan aikin da aka yimasa na siyomasa kayan, ko kuma a fadamasa cewa wannan abinda kace a siyoma zan siyoshi sannan na siyarma dashi, idan ya yarda to , ragin da aka samu na mai siyowane hakama zai iya sakamasa riba.
Malamai suna cewa : koda kyauta mai siyar da kayan ya baka, to, hakkin Wanda ya baka sautu ne ba taka bace. hakama ragi.
مطالب أولى النهى (3/132)Don haka idan aka karawa mai siyan kudi a matsayin riba, ba'ayi gaskiya ba kuma bai halatta ayi karya ba cikin mu'amala da cin dukiyar mutane babu hakki.
Don haka a lazumci gaskiya hakan zai saka a sami albarka cikin kasuwanci Kamar yanda ya faru lokacin da manzon Allah sallalahu alaihi wasallam ya aiki Urwatul Barikiy ya siyomasa dabbar layya, da yaje sai ya sami dabbobi biyu a dinari daya, a hanyar dawowarsa sai ya hadu da wani ya siyar masa da guda daya a dinar guda, ya kawowa manzon Allah dinar daya da akuya guda daya, sai yayiwa manzon Allah bayanin abinda ya faru sai manzon Allah yayimasa addu'ar : Allah yayimasa albarka a harkar kasuwancinsa.
Allah ne mafi sani.
*✍📚Shashen fatawa a bisa Qur'ani, Sunnah da maganganun magabata na ƙwarai (sawtul hikmah)*
18/1/1400.
17/09/2019.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Proză scurtă*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: