*INA YIN CHARTING DA WANDA BA MIJINA BA, MENE HUKUNCINA

161 4 0
                                    

*056 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*INA YIN CHARTING DA WANDA BA MIJINA BA, MENE HUKUNCINA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum Malam, mace ce tana da aure sai kuma wani daban wanda ba mijinta ba yana koya mata karatu ta whasapp, to malam meye hukuncinsu ya halalta su yi ko kar su yi? Nagode.

AMSA:

Wa'alaikumus Salam. A gaskiya wannan babban kuskure ne suke aikatawa, saboda wannan mataki ne na kaiwa zuwa ga aikata ba daidai ba, domin in dai malamin ya amsa sunansa malami, to shi ma ya san wannan kuskure ne, domin yawan hulɗa da mace a inda babu muharraminta, zai iya haifar da afkawa ga saɓon Allah, ko da kuwa hulɗa ce ta addini, saboda hadisin da Bukhariy ya ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas, Annabi ﷺ ya ce: "Kada wani mutum ya keɓanta da wata mace face sai da muharraminta". Bukhariy 4955.

Saboda haka ta ji tsoron Allah ta dakatar da wannan karatu, ta koma makaranta wurin malamai don yin karatu na haqiqa, WhatsApp da Facebook ba shi ne wurin da ya kamata a ce ta mayar da shi makaranta na haqiqa ba, saboda ba wurin kowane malami ne ake ɗaukar karatu ko ilimi ba, saboda yadda rayuwa ta gurɓace a wannan lokaci da muke ciki. Kuma na tabbatar matuqar mijinta ya san haka ba zai ji daɗi ba, kuma ba zai yarda da hakan ba, wannan ke qara nuna cewa wannan tsarin karatu ba daidai ba ne.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
30/5/1440 h.
05/02/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now