*TAMBAYA TA 130*
*LITTAFIN ‘Al-MA’ATHUURAAT’*
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah,
Muna amfani da littafin Azkaar na Al-Ma’athuuraat, amma sai aka ce wai akwai abubuwan da ba su inganta ba a cikinsa. Ko malam zai taimake ni da wuraren da ba su ingantan ba, in akwai?
AMSA A130:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
A gaskiya, babu wani littafin da babu matsala a cikinsa, ban da Littafin Allaah Alqur’ani, sai kuma littaffan da suka tattara Sunnah Sahihiya, waɗanda kuma al’umma ta haɗu a kan sahihancinsu, kamar Sahih Al-Bukhaariy da makamantansa.
Don haka, malamai a kullum suke ta yin aikin takhreej mai ƙunshe da bayanin darajar kowace riwaya a kan littaffan, watau: Ware sahihai daga raunana na riwayoyin da suka zo a cikin littaffan. Sai dai ban san wani malamin da ya yi wa Littafin Al-Ma’athuuraat irin wannan aikin ba.
Don haka, maimakon Al-Ma’athuuraat gara ku yi amfani da littafin Hisnul Muslim Min Azkaaril Kitaab Was Sunnah na As-Shaikh Al-Qahtaaniy (Rahimahul Laah). Ban san wanda ya kai shi ba a nan kusa, sai dai ko Sahih Al-Azkaar da aka tattaro daga littaffan Al-Imaam Al-Albaaniy ko wanda As-Shaikh Al-Adawiy ya wallafa, sai dai kuma suna da yawa ne.
Wal Laahu A’lam.
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
29/8/2019
1: 56pm.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: