*HUKUNCIN YI WA MAMACI LAYYA

208 0 0
                                    

*199 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*HUKUNCIN YI WA MAMACI LAYYA*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam. Allah ya yi wa mahaifina rasuwa ina bukatar addu'arku . Sannan zan iya yin layya da niyyar Allah yakai Masa ladar layyar?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, ƴar uwa muna yi wa mahaifinki addu'ar Allah ya jiqan sa ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma lulluɓe shi da rahamarsa, da sauran duk Musulman da suka gaba ce mu.

Yi wa mamaci layya ba tare da ya yi wasiyya ba, yana daga cikin masá'il da malamai suka yi saɓani a kai, sai dai mafi yawan malamai sun karkata a kan halascin yi wa mamaci layyar.

Saboda ya tabbata Nana A'isha ta ruwaito hadisi cewa Manzon Allah ﷺ an zo masa da rago ya yi layya da shi, a lokacin da zai yi layyar sai ya ce: "Bismillah, ya Allah ka karɓa daga Muhammad da Iyalan Muhammad da kuma al'ummar Muhammad".
Muslim 1967.

Sanannen lamari ne cewa daga cikin al'ummar Annabi Mihammad ﷺ akwai mamata, sai ga shi Manzon Allah ﷺ ya sa su a cikin layyar da ya yi, a nan sai malamai suka ce wannan ya nuna halascin yi wa mamaci layya. Sananan malamai sun bayyana cewa mamaci na amfana da sadakar da aka yi masa, saboda haka layya ga mamaci sadaka ce daga cikin sadakoki, ana fatan in Allah yarda mamaci zai amfana da sakamakon sadakar.

Amma duk da haka ba a ruwaito cewa Annabi ﷺ ya duqufa da yi wa mamata layya duk shekara ba, in da a ce abu ne da za a yi ta yi a duk shekara da an ruwaito cewa Annabi ﷺ ya duqufa a kai, sai dai ya halasta a yi ba tare da dauwama a kan haka duk shekara ba.

Domin qarin bayani duba ALMAJMÚ'U (8/406 - 407). Ko a duba Maɗálibu Ulin-Nuhá (2/472).

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
5/12/1440 h.
06/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now