*BAYANI AKAN SALLOLI BIYAR NA FARILLA?*

616 4 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*BAYANI AKAN SALLOLI BIYAR NA FARILLA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Dan ALLAH ina so a kara mana bayani sossai yadda ake salloli 5 na farillah.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, Da farko ba a yin sallah sai da tsarkin jiki da na tufafi da muhallin yin sallah, haka nan ba a yin sallah sai da alwala, ko taimama a inda aka rasa ruwan yin alwala ɗin. Kuma ba a yin sallah sai lokacinta ya shiga, duk wanda ya yi sallah kafin shigar lokacinta sallarsa ba ta yi ba sai inda shari'a ta amince da hakan. Kuma babu sallah ga wanda bai yi kabbarar harama ba, kuma kabbarar harama a tsaye ake yinta.

Sannan kuma babu sallah ga wanda bai yi karatun Fatiha a cikinta ba kamar yadda hadisi ingantacce ya tabbatar, duk raka'ar da mutum ya yi bai karanta Fatiha a cikinta ba, to ba shi da wannan raka'ar sai ya sake yin wata raka'ar a madadinta.

Duk wanda ya mnace ya rage wani aiki daga cikin ayyukan sallah, ko ya mance ya qara wani aiki daga cikin ayyukan sallah, to ba sallamewa ake a sako farko ba, ana gyara ta ta hanyar yin sujjada biyu kafin sallama ga wanda ya rage wata sunnah ko sunnoni, ko a yi sujjada biyu bayan sallama ga wanda ya qara wani aiki. Za a sami cikakken bayani idan aka tuntuɓi malamai.

Sallolin farilla guda biyar ne a kowace rana, ga su ɗaya bayan ɗaya:

1. AZUHUR: Tana da raka'o'i guda huɗu, raka'o'i biyu na farko ana karanta Fatiha da Sura a asirce, sai a zauna a yi zaman tahiya, a miqe a ciko raka'o'i biyun qarshe, su kuma ana karanta Fatiha ne kaɗai ba Sura, idan kuma aka mance aka karanta sura a cikinsu ba komai. Bayan an gama su sai a zauna a sake yin tahiya a yi sallama.

2. LA'ASAR: Ita ma raka'o'i huɗu take da su kamar na Azuhur ɗin can, kuma iri ɗaya ake yinta da yadda ake yin Azuhur ɗin.

3. MAGRIBA: Ita kuma raka'o'i uku take da su, raka'o'i biyun farko ana karanta Fatiha da sura a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, a miqe a ciko raka'a ta uku, amma ita ana karanta Fatiha ce kaɗai a asirce, sai a sake zaman tahiya a yi sallama.

4. ISHA'I: Ita kuma raka'o'i huɗu take da su kamar na Azuhur da La'asar, sai dai bambancinta da su shi ne; raka'o'inta biyu na farko ana karatu a cikinsu ne a bayyane ba a asirce ba.

5. ASUBAHI: Ita kuma tana da raka'o'i biyu ne kacal, kuma ana karanta Fatiha da sura a cikinsu ne a bayyane, har ma an so a ɗan tsawaita karatu a cikin raka'o'inta fiye da na sauran sallolin. Duka wannan dai a taqaice ne.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
25/6/1440 h.
02/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now