*Tambaya ta 009:*
*YA SIFFANTA MATARSA DA MAHAIFIYARSA*
_Assalamu Alaikum,_ malam.
Barka da rana, yaya aiki? Allah ya yi mana jagoro, ya saka maka da alkhairi.
Malam, don Allah ya hukuncin auren da miji ya ce da matar, yana mata kallon Kirista saboda irin ɗabi’unta? Sannan kuma ya ce, yana mata kallon uwarsa: Yadda ba zai haɗa gado da uwarsa ba, haka ita ma ba zai haɗa shimfiɗa da ita ba?!
*AMSA A009:*
_W alkm slm w rhmt laah._
1. Yana daga cikin haƙƙoƙin mace a kan mijinta, ya kiyaye harshensa a kanta, kar ya riƙa munana mata a wurin zagi ko aibatawa.
Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:*سِبَابُ الْمُسْلِمِ فُسُوقٌ ، وَقِتَالُهُ كُفْرٌ*
*Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙi da shi kafirci ne.*Kuma an taɓa tambayar Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ game da haƙƙin matar ɗayanmu a kansa? Sai ya ce:
*أَنْ تُطْعِمَهَا إِذَا طَعِمْتَ، وَتَكْسُوهَا إِذَا اكْتَسَيْتَ، وَلَا تَضْرِبِ الْوَجْهَ، وَلَا تُقَبِّحْ، وَلَا تَهْجُرْ إِلَّا فِي الْبَيْتِ*
*Shi ne: Ka ciyar da ita idan ka ci, ka tufatas da ita idan ka tufatu, kar ka bugi fuska, kar ka munana, kuma kar ka ƙaurace sai a cikin ɗaki* .*2. Sannan kuma kamanta ta da kirista babban abu ne mai hatsarin gaske, domin zai iya ɗaukar ma'anar kafirtawa. Abu ne sananne kuwa cewa, duk lokacin da wani ya kira ɗan'uwansa da kalmar 'kafiri', to ɗayansu ya komo da ita, kamar yadda ya zo a cikin Hadisi sananne daga bakin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)._ Allaah Ta'aala ya kiyaye.
3. Amma kamanta ta da mahaifiyarsa shi ake kira: *Zihaari* , wanda Allaah Ta'aala da kansa ya siffata masu yinsa da cewa:
*وَإِنَّهُمْ لَيَقُولُونَ مُنْكَرًا مِنَ الْقَوْلِ وَزُورًا*
*Kuma lallai ne, suna faɗin abin ƙyama na magana, kuma da ƙiren ƙarya.*4. Don haka, abin da ya wajaba ga mai aikata wannan shi ne: Bayan *tuba* da *istigfari* sai kuma dole ya yi *Kaffara* :
Ya nemi baiwa ya 'yanta ta; in kuwa ba zai iya ba sai ya yi azumin watanni guda biyu a jere; idan kuma ya kasa, to sai ya nemo talakawa guda sittin ya ciyar da su.
5. Sannan kuma dole ne ya fara yin wannan kaffarar tun kafin ya ƙara komawa ga saduwa da matar, kamar yadda Allaah Maɗaukakin Sarki ya ambata a farkon *Suratul Mujaadalah.*
_Wal Laahu A'lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
29 - 1 - 2018
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: