*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*NA SHA AZUMI SABODA SHAYARWA, CIYARWA ZAN YI KO RAMAWA?*
TAMBAYA:
Assalamou aleikoum, malam ina tambaya, ni che na kasanche na haifou wata daya kafin Ramadan, da ramadan ya zo ban yi azoumi ba, ban ma gwada ba ballantana in ga zan iya ko kouwa, kawai sai na fake da chiyarwa ban yi azoumin ba, to malam ramkachi zan yi ko chiyarwa zan yi?
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, Game da hukuncin mace mai ciki da mai shayarwar da suka sha azumi, malaman Musulunci sun yi saɓani game da abin da ke kansu na hukunci, shin ciyarwa za su yi kaɗai, ko ramawa kawai, ko kuma ciyarwa da ramawa?
Waɗannan zantuttuka guda uku, wanda ya fi rinjaye a cikinsu shi ne: Lallai mai ciki da mai shayarwa idan suka sha azumi, to za su ciyar da miskini ɗaya ne kawai a madadin kowane azumi ɗaya, babu ramuwa a kansu, saboda sun shiga qarqashin faɗin Allah da yake cewa: "Abin da ke kan waɗanda ba sa iya azumi shi ne ciyar da miskinai" Suratul Baqara, aya ta 184.
Don ganin wannan bayani duba FATAÁWAS SIYAM, WA FATAÁWÁ MU'ÁSIRA, shafi na 170, na Mahmud Almisriy.
Ko a duba ALMUGNIY 3/149 na Abdullahi Ibn Qudama don qarin bayani.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
16/Ramadan/1440 h.
21/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: