*189 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*YA MATSAYIN MIJI MAI BAMBANTA RABON KWANA A TSAKANIN MATAYENSA?*
TAMBAYA:
Asslamu Alaikum malam Dan Allah inada tambaya .
Abokan zamana sun yi tafiya sun tafi garinsu watan su daya sai ya dawo gidana da zama sai ya ke ce min in sun dawo zai je can ya yi wata daya a gunsu, shin malam an mini adalci ba a shiga hakkina ba ko hakane ne daidai? Saboda ni ma na taba tafiya sati uku ko da na dawo ko kwana daya ba a kara min ba.AMSA:
Wa'alaikumus Salam, wajibi ne a kan mijin da ke da mata fiye da ɗaya ya yi adalci a tsakanin matayensa ta hanyar rabon kwana, da abinci da wurin zama. Rashin yin adalci a cikin waɗannan abubuwa ko shakka babu zalunci ne, wanda kuma Allah ba zai kyale hakan ba.
Duk matar da ta yi tafiya na wasu kwanaki ko watanni, to ba sharaɗi ba ne a ce idan ta dawo sai an rama mata waɗannan kwanakin da ba ta nan, idan kuma aka ce sai an rama mata to an cutar da sauran matayen ko ɗaya matar idan su biyu ne. Saboda haka kuskure ne babba miji ya rama wa matar da ta yi tafiya kwanakin da ba ta nan, lallai wannan ba dai-dai ba ne, duk matar da ta yi tafiya har zagayowar kwananta ya shuɗe ba ta nan, to haqqin wannan kwana ko kwanaki sun faɗi, ba wata maganar ramuwa, wannan shi ne adalci.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
28/11/1440 h.
31/07/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: