*005 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SU WANE NE FUQAHA’US SAHABA?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahmatullah, Don Allah Malam Ina da Tambaya a makaranta aka ba mu mu nemo, tambayar ita ce kamar haka: suwane ne fuqahabus sahaba?
AMSA:
Wato idan aka ce Fuqaha'us Sahaba, ana nufin malaman Fiqhu masu bayar da fatawa daga cikin Sahabban Manzon Allah s.a.w. Daga cikin manyan malaman Fiqhu na Sahabban Manzon Allah s.a.w. akwai halifofin nan guda huɗu, wato Sayyiduna Abubakar Assiddeeq da Umar ɗan Khaɗɗab da Usman ɗan Affan da Aliyu ɗan Abu Ɗalib Allah ya qara masu yarda.
Bayan waɗannan huɗun kuma sai Abdullahi ɗan Mas'ud, da Zaidu ɗan Tsabit, da Abu Musal Ash'ariy, da Mu'azu ɗan Jabal, da Ubayyu ɗan Ka'ab, da Abud Darda'i, da Uwar Muminai A'isha 'yar Abubakar, da Abdullahi ɗan Abbas, da Abdullahi ɗan Umar, da Abdullahi ɗan Zubairu ɗan Auwam, da kuma Abdullahi ɗan Amru ɗan As Allah ya qara masu yarda baki ɗaya.
Waɗannan suna daga cikin fuqaha'us Sahaba, wato Sahabban Annabi s.a.w. sukan nemi fatawoyi a wurinsu a kan lamuran addini a duk lokacin da suka buqaci hakan. Sai dai waɗannan ba su kaɗai ne fuqaha'us Sahaba ba, akwai wasu da dama irinsu Nana Faɗimatu 'yar Manzon Allah s.a.w, da Hafsa 'yar Umar, da su Ɗalhatu ɗan Ubaidullah, da sauransu da dama da ba a lissafo su a nan ba, Allah ya qara masu yarda.
Dubi 'DABAQAATUL FUQAHA’I shafi na 35 zuwa 52, na Jamalud Deen, Ibrahim ɗan Aliyu ɗan Yusuf.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
3/4/1440 H.
10/12/2018 M.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Cerita Pendek*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: