*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN MAZIYYI YANA BATA AZUMI?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum, Shin wai malam maniyi ne kadai ke karya azumi ko kuma har da maziyyi? Nagodeb
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, Malamai sun yi saɓani game da hukuncin mai azumin da ya fitar da maziyyi, daga cikin malamai akwai masu fahintar duk mai azumin da maziyyi ya fito masa, to azuminsa ya karye. Amma wasu malaman kuma suka ce azumin sa bai karye ba, saboda maziyyi ba ya wajabta yin wankan tsarki, matsayinsa kamar na fitsari ne, don haka duk mai azumin da maziyyi ya fito masa azuminsa yana nan.
Duba Almajmu'u Sharhul Muhazzab 6/323.
Amma yana da kyau mai azumi ya kiyaye kalle-kalle da tunane-tunanen abubuwan da za su sa shi ya kai ga wannan mataki.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
13/Ramadan/1440 h.
18/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Cerita Pendek*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: