*'ALLAHU AKBAR' YAKE FAƊI A YAYIN ƊAGOWA DAGA RUKU'U

300 3 0
                                    

*Tambaya ta 013:*

*‘ALLAHU AKBAR’ YAKE FAƊI A YAYIN ƊAGOWA DAGA RUKU'U*

_Assalamu Alaikum,_ don Allaah tambaya ce da ni:

Menene hukuncin mutumin da yake jan mutane limanci a sallah, amma a wajen ɗagowa daga ruku'u sai ya ce: *‘Allahu Akbar’* a maimakon ya ce: *‘Sami'al Laahu Li Man Hamidah.’*

Sannan kuma menene hukuncin faɗin: *‘Sami'al Laahu Li Man Hamidah’* a sallah?

*AMSA A013:*

_W alkm slm w rhmt laah._

[1] Da farko wajibi ne kowannenmu ya san cewa abin da ya tabbata a SunnahSSahihiya, kuma malamai suka yi *ittifaaqi* a kansa shi ne:

Duk lokacin da liman ko mai Sallah shi kaɗai yake ɗagowa daga ruku'u sai ya ce: *'Sami'al Laahu Li Man Hamidah'.* Idan kuma ya daidaita a tsaye sai ya ce: *'Rabbanaa Lakal Hamd'* ko *'Rabbanaa Wa Lakal Hamdu'* ko *'Allaahumma Rabbanaa Lakal Hamdu'* ko *'Allaahumma Rabbanaa Wa Lakal Hamdu.'*

[2] Amma game da mamu mai Sallah a bayan liman ne malaman suka sha bamban. Kuma abin da ya fi bayyana, kuma ya fi zama daidai a fahimtarmu daga cikin maganganunsu shi ne:

Shi ma dai yadda limaminsa ya yi haka zai yi, watau ya faɗi *'Sami'al Laahu Li Man Hamidah'* a lokacin ɗagowa, kuma ya faɗi *'Rabbanaa Wa Lakal Hamdu'* bayan ya gama ɗagowa. Saboda Hadisin Al-Bukhaariy wanda a cikinsa Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:

*صَلُّوا كَمَا رَأَيْتُمُونِي أَصَلِّي*
*Ku yi Sallah kamar yadda kuka ganni ina yin sallar.*

Kuma da wanda ya ce:

*إِنّمَا جُعِلَ الْإِمَامُ لِيُؤْتَمَّ بِهِ*
*An sanya Liman ne kaɗai domin a yi koyi da shi.*

Kuma amma game da hadisin da ya ce:

إِذَا قَالَ ألْإِمَامُ : *(سَمِعَ اللهُ لَمَنْ حَمِدَهُ)* فَقُولَوا : *(رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ)*
Idan Liman ya ce: ' *Sami'al Laahu Li Man Hamidah'* sai ku ce: *'Rabbanaa Wa Lakal Hamdu'*

Malamai irinsu Al-Imaam As-Suyuutiy a cikin *Al-Haawiy Lil Fataawiy* sun nuna cewa, bai saɓa wa abin da ya gabata ba, saboda wasu bayanai ingantattu da ya zo da su a can.

Game da hukuncin faɗin *'Sami'al Laahu Li Man Hamidah'* kuwa, abin da ya fi bayyana daga maganganun malamai shi ne: Shi *wajibi* ne, ko kuma *Sunnah Mu'akkadah* domin hadisin da Al-Imaam Abu-Daawud ya riwaito daga hadisin mutumin nan Mai Munana Sallarsa, inda Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya umurce shi da faɗin wannan zikirin a lokacin ɗagowa daga ruku'u.

Don haka, limamin da ba ya faɗin wannan zikirin a lokacin ɗagowa daga ruku'u, kuma yake musanya shi da wani zikirin daban, sai a ce ya kayar da wannan wajibi kenan daga cikin sallarsa. Kuma dole a yi masa nasiha domin ya gyara.
Idan kuma ya ƙi yarda da nasihar, ya cigaba da wannan ɓarnar, to sallarsa tana iya ɓaci, saboda wulaƙanta surar sallar da ya yi.

Wanda ya yi Sallah a bayan irin wannan limamin sallarsa ta yi, matuƙar dai shi ya faɗi abin da yake daidai a lokacin ɗagowarsa da lokacin tsayuwarsa, saboda hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito cewa Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:

Suna yi muku limanci; to idan suka dace, duk kun dace. Idan kuwa suka yi ba daidai ba, to kun dace, su kuma sun kauce wa daidai.

_Wal Laahu A'lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
6 - 2 - 2018

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now