*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SIFFAR AIKIN UMRA A TAQAICE*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum, malam don Allah yaya ake yin aikin Umura?
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, aikin Umra ibada ce da musulmi yake da damar zuwa ya je ya aikata a duk ranakun shekara a fahimtar jumhurun malaman Musulunci, amma yin ta a lokacin Ramadana yana da fifiko a kan sauran lokutan, saboda maganar Manzon Allah ﷺ da ya ce: "Umra a Ramadana tana dai-dai da Hajji".
Bukhariy 1782, Muslim 1256.Aikin Umra yana da rukunnai guda uku kamar haka:
1. Ihrami.
2. Ɗawafi
3. Sa'ayiDuk wanda ya bar rukini ɗaya ɗaga cikin waɗannan rukunnai, to aikinsa bai kammalu ba.
Da farko dai wajibi ne ga mai aikin Umra ya qulla ihrami daga miqati, idan ya kasance zai wuce ta miqati ɗin ne, amma idan ba ta miqati zai wuce ba, to zai ɗaura ihraminsa ne daga gidansa, miqatin mutanen Afrika shi ne Juhfa, idan an zo wajen shugabannin tafiya sukan sanar. Ihrami na nufin qulla niyyar aikin Umra ko Hajji, miqati kuma shi ne wurin da mai nufin aikin Hajji ko Umra ke qulla niyya. An so a lokacin da maninyaci ya ɗauki harama ya ce: 'LABBAIKALLAHUMMA UMRATAN', kuma an so maninyaci ya yi wankan shiga Makka, mace ce ko namiji.
Daga nan idan namiji ne sai ya sanya kayan harami, amma idan mace ce za ta sa kayanta ne na yau da kullum kawai.
Sai maninyaci ya fara yin TALBIYYA, idan namiji ne zai ɗaga sautinsa, mace kuma za ta ɗan yi qasa-qasa da sautinta, ta yadda na gefenta ne kawai yake jin Talbiyyarta, Talbiyya ita ce: LABBAIKALLAHUMMA LABBAIK, LABBAIKA LASHAREEKA LAKA LABBAIK, INNAL HAMDA, WANNI'IMATA, LAKA WALMULK, LÁSHAREEKA LAK.
Sai kuma yin ɗawafi, wato kewaya ɗakin Ka'aba mai girma kewaye bakwai, ana farawa ne daga Hajarul Aswad, kuma ana qarewa ne da Hajarul Aswad ɗin, a lokacin da maninyaci yake ɗawafi zai sa Ka'aba a ɓangarensa na hagu ne, bayan ya gama ɗawafi sai ya yi sallah raka'a biyu a bayan Maqamu Ibrahim idan ya sami dama, idan kuma bai sami dama ba ya yi a ko'ina ya samu dama a cikin Harami, a raka'a ta farko bayan Fatiha zai karanta suratul Kafirun, a raka'a ta biyu kuma bayan Fatiha zai karanta suratus Samad (wato Qulhuwallahu Ahad). In ya sami dama sai ya sha ruwan Zamzam.
Sannan sai ya yi sa'ayi tsakanin Safa da Marwa zagaye bakwai, zai fara ne daga Safa, sai ya qare da Marwa.
Daga nan sai ya aske gashinsa idan namiji ne ko ya yi saisaye, amma askewa shi ya fi, idan kuma mace ce ba aske kan za ta yi ba, za ta cire gwargwadon girman kan ɗan yatsa inda qumba yake ne a gashin kanta. Bayan haka kuma sai maninyaci ya ziyarci Madina.
Wannan ita ce siffar aikin Umra a taqaice, ana iya tuntuɓar malamai don su qara fitowa da bayanin sarari, Allah ya sa mu dace, amin.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
17/7/1440 h.
24/03/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: