*HANYOYIN DA MUTUM ZAI BI DOMIN KARE KANSHI DAGA ZINA*
*Tambaya:*
Malam ni mutum ne mai karfi da kuma yawan sha'awa .
Wannan yasa wani lokaci shaidan ke riya mani inje in aikata zina don in samu saukin sha'awar gashi kuma ni yaro ne karami ban wuce shekara Ashirin ba shine nike neman malam ya taimaka mani da shawarwari da zan bi don ganin na magance wannan matsalar.*Amsa:*
Sha'awa a jikin ďan adam ďabi'a ce, amma Allah yai ma bayinsa hanyoyin da za su bi domin mu'amala da ita. Saboda haka qarfin Sha'awa ba matsala ba ce; sai dai idan an yi amfani da ita ta yadda bai dace ba.
A matsayinka na matashi mai qarfin Sha'awa ana baka shawarar bin waďannan hanyoyi:*1-* Qoqarin yin aure domin shi ne magani na qarshe na qarfin Sha'awa.
*2-* Yawaita azumi; domin Annabi ya faďe shi a matsayin makwafin aure ga wanda bai da ikon yin auren.
*3-* Nisantar duk wani abu da zai motsar maka da sha'awa, kamar: kallace-kallace, da yawan tunane-tunane.
*4-* Zama da mutanen Kirki.
*5-* Nisantar zama kai kaďai.
Allah ya taimake ka ya sa ka kub'uta daga wannan jarabawa.
*Amsawar: ✍*
*Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria {Hafizahullah}.*
17 Zhul-qa'adah, 1439H
{31 Yuli, 2018M}.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: