TAMBAYA 1,303
Mlm mace ne bayan tayi tsarki daga al,adanta to sae akwai kayan data saka alkcn al,adarta sae tayi sallan asubah da kayan sae tacire su washe gari kuma mah takuma yin asubar dasu sannan tacire to sae wajen axahar ta wnn ranar kawai sae taga wnn kayan datayi sallar asuba dasu sau biyu akwai digo digon wnn jinin al,adar ajiki to mlm ya matsayin wnn sllar asubar guda biyu datayi da wnn kayan
AMSA
Sallah tayi saboda ai bata sani bane cewa tufafin da jini ,saboda hadisin annabi (saw) wanda mala'ika jibrin yazo ya same shi da sahabbai suna salla kowa da takalminsa a ƙafarsa , sai aka ga annabi ya cire takalminshi sai sahabbai ma suka cire nasu bayan ya gama sallar sai ya tambayesu mai yasa suka cire takamansu sai suka ce ai sunga ya cire nashi ne, sai yace ni mala'ika jibril ne ya sanar dani cewa ƙarƙashinsu akwai najasa, don haka idan ɗayanku yazo zaiyi salla da takalmansa to ya duba ƙasansu idan da najasa ya goge, kuma ba a samu wata riwaya da ta nuna cewa annabi ya biya wannan sallar da ya sallata da takalaminsa mai najasaba , da wannan malamai ke cewa duk lokacin da mutum yayi salla da najasa a jikinsa bai sani ba sai daga baya ya gani sallarshi tayi ba sai ya sake ba.
Wannan bayani na cikin fiqhul ibadat da sheikh uthaimin da fatawarsa, da fatawa ibn baaz, da fiqhussunah na saidussabiq a juz'i na 1.
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam DaiyibTAMBAYA 1,302
slm Malam tambayana anan ME hukuncin Mijin dayake Jima,i da matar sa tana halin jinin haila
AMSA
wannan na daga cikin manyan zunubai da annabi yace Allah ya tsinewa mai aikatawa, sannan duk wanda yayi irin wannan ɓarna yana iya samun fushin Allah, sannan dukkan jikin mace an baka dama ka mora idan banda gabanta, sannan ya halatta ta biyawa namiji buƙata da sassan jikinta har ya gamsu, kuma mai irin wannan aikin yana cikin ƙazamai saboda shi al'ada lalataccen kwai ne yake zubewa wanda yana tattare da kwayoyin cuta wanda suna haddasawa namiji matsaloli dayawa a jikinsa, don haka haƙura zuwa lokacin tsarkin mace yafi kwanciyar hankali.
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: