YIN ADDU'A DA HAUSA A CIKIN SALLAH

849 2 0
                                    

Tambaya ta 112

YIN ADDU’A DA HAUSA A CIKIN SALLAH

As-Salaam Alaikum.

Malam, wani ne ya ce wai malamai sun bayar da fatawar cewa ya halatta mutum ya yi addu’a da Hausa a cikin sallah. Ni kuma na ce, gaskiya ban taɓa ji ba! Shi ne nake tambaya?

AMSA A112:

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] Kamar yadda na faɗa a farkon amsar tambaya: *A109:* Ba abin mamaki ba ne a samu bambancin fatawa a kan mas’alolin fiqhu, saboda bambancin mahangar da malamai suke duban mas’ala ta cikinsu.

Muhimmin abu dai shi ne: Kowannensu ya ji tsoron Allaah, kuma ya gina bincikensa da maganganunsa a kan tubali ƙaƙƙarfa na ilimi, ba son-zuciya ko bin sha’awar-rai ko shaci-faɗi ba.

Babu wani malami guda a bayan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya zama tsararre daga yin kuskure, ko mantuwa, ko zamiya a cikin maganganunsa na ilimi.

Don haka, dole ne duk malami na-Allaah ya zama cikin shirin karɓar gyara daga duk inda ta fito, matuƙar dai kuskurensa a cikin maganganunsa da fatawoyinsa sun bayyana.

[2] Nau’ukan addu’a a cikin Sallah iri biyu ne: Akwai *Du’aa’ul Mas’alah* da kuma *Du’aa’ul Ibaadah.*

Na-farkon shi ne wanda a cikinsa akwai nema da roƙon Allaah a fili cewa ya biya wata buƙata, ko dai ta hanyar tunkuɗe wani sharri, ko kuma ta hanyar janyo wani amfani ga mai yin addu’ar. Alal misali: *Addu’ar Buɗe Sallah* mai lafazin:

اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ ؛ كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ ، اللَّهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدِ
Ya Allaah! Ka nisantar da abin da ke tsakanina da kura-kuraina, kamar yadda ka nisanta a tsakanin Gabas da Yamma! Ya Allaah! Ka tsaftace ni daga kura-kuraina, kamar yadda ka tsaftace farar tufa daga datti! Ya Allaah! Ka wanke ni daga kura-kuraina da ruwa da ƙanƙara manya da ƙanana.

Amma *Du’aa’ul Ibaadah* kuwa ita ce, wadda a cikinta babu roƙo ko neman wata buƙata a fili daga Allaah Maɗaukakin Sarki, sai dai kawai karanta kalmomin girmamawa da kambama Ubangiji Ta’aala, kamar wani lafazin na addu’ar Buɗe Sallaah, cewa:

سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ ، وَتَعَالَى جَدُّكَ ، وَلَآ إِلَهَ غَيْرُكَ
Ya Allaah! Tsarki ya tabbata gare ka haɗe da godiyarka; kuma Sunanka ya yi albarka; kuma martabarka ta ɗaukaka; kuma babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai kai!

[3] Sannan yawancin wuraren da ake yin karatu a cikin sallah sanannu ne, kuma kafaffu ne, waɗanda mutum ba shi da ikon sauya su, ya zo da waɗanda ba su ba, kamar haka:

1. Bayan kabbara kafin a fara karatu: *Addu’o’in Buɗe Sallah.* Kafaffu ne.

2. A tsaye kafin Ruku’u: *Karatun Fatihah da Surah.* Kafaffu ne.

3. A bayan Fatihah: *Ameen.* Kafaffe ne.

4. Addu’a don kawar da waswasi: *Isti’azah.* Kafaffiya ce.

5. A cikin ruku’u: *Zikirori da Addu’o’i.* Kafaffu ne.

6. Dagowa daga ruku’u: *Zikiri* ne kafaffe.

7. A cikin Sujada: *Zikirori da Addu’o’i.* Kafaffu ne.

8.  A zama tsakanin sujada-biyu: *Zikirori da Addu’o’i.* Kafaffu ne.

9. Kafin ruku’un raka’ar ƙarshe: *Qunuut na Wutri* , kafaffe ne.

10. Bayan ruku’un raka’ar ƙarshe: *Qunuut na Naazilah* , ba kafaffe ne. Amma yana dacewa da yanayi ne.

11. Zaman Tahiya: *KaratunTahiya,* kafaffe ne. *Addu’ar neman tsari daga sharrin abubuwa huɗu,* kafaffe ne. Sauran *addu’o’i da zikirori* kafin sallama, kafaffu ne.

Daga nan an fahimci cewa:

(i) Yawancin wuraren yin addu’o’i a sallah kafaffu ne, mutum ba ya iya zuwa da wata addu’arsa ta musamman a tare da su, ko a maimakonsu.

(ii) Addu’o’in Al-Qunuut da aka ce ana iya ƙarawa, ana ƙarawa da abin da ya dace da yanayin da ake ciki ne. Kuma da Larabci ake yi, ba da wani yare kamar Hausa ba.

(iii) Ko a cikin Sujada da aka riwaito cewa: *Ku yawaita yin addu’a a cikinsa,* da kuma Zaman Tahiya da aka riwaito cewa: *Sannan sai ya zaɓi addu’ar da ya fi so ya yi* , manyan malamai irinsu Al-Imaam Ahmad sun zaɓi cewa:

Ma’anarsa ita ce: Ku zaɓo daga cikin waɗanda suka inganta daga Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)._

Kuma duk mun san cewa: Ba da Hausa Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi addu’o’insa ba.

[4] Sannan kuma ga Sahabi Mu’awiyah Bn Al-Hakam _(Radiyal Laahu Anhu)_ wanda ya gai da mai atishawa a cikin sallah a masallaci. Daga baya kuma Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya kira shi, ya gaya masa cewa:

*Wannan sallar, babu wani abu na maganar mutane da ke gyara ta. Ita dai tilawar Alqur’ani ce da zikirin Allaah kawai.*

Idan kuwa har yin maganar Sahabi da harshen Larabci a cikin sallah za a nuna cewa ba ya gyara sallah, to ina kuma ga wanda ya yi da wani yaren da ba Larabcin ba, kamar Hausa?!!

[5] Kuma idan muka yarda da cewa, ya halatta a yi addu’a a cikin sallah da Hausa saboda hujjar wai mai yin addu'ar bai iya Larabci ba, to ranar da wani ya zo da cewa, ya halatta a yi karatun *Fatihah* ko *Surah* a cikin sallar da harshen Hausa ko Fulatanci ko wani harshen da ba Larabcin ba, saboda irin wannan dalilin cewa bai iya Larabci ba, me za mu ce masa?!

[6] Tun da akwai sauran wuraren da Shari’a ta bayyana cewa ana karɓar addu’a a cikinsu, waɗanda ba cikin sallah su ke ba, kamar: A tsakanin kiran sallah da iqamah; da ƙarshen dare; da lokacin saukan ruwan sama; da lokacin da musulmi ke cikin tafiya; da ranar Jumma’a, musamman daga bayan la’asar kafin faɗuwar rana, da sauransu. Meyasa musulmi ba zai yi addu’a a waɗannan lokutan da yarensa ba? Meyasa zai nace sai ya yi addu’a da yarensa a cikin sallah, ta yadda zai iya samun matsala dangane da sallarsa?

[7] A ƙarshe: Kar mu manta: Wanda ya bayar da fatawa a kan halaccin hakan, ba fa wata aya ko hadisi ya janyo a fili ƙarara mai nuna halaccin hakan ba, a iya saninmu. Illa dai kawai a fahimtarsa da addini ne yake ganin babu matsala idan musulmi ya yi addu’a da yarensa a cikin sallah! Shi ne muke cewa:

Idan aka tafi Lahira kuma ya zama an samu matsala fa?!

Don gudun hakan gara dai mutum ya nisanci saka kalmomin da ba daga harshen Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ suka fito ba, a cikin sallarsa.

Wannan fahimtarmu kenan a kan wannan mas’alar a yanzu. Wanda ya zo da hujjar da ta fi wannan a shirye mu ke, mu karɓa daga gare shi, kuma mu sauya matsayinmu, _in shaa’al Laah._

_Wal Laahu A’lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
22/7/2019
3: 23pm.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now