*TAMBAYA TA 094*
*KYAUTATA WA IYAYE A BAYAN AURE*
_As-Salamu Alaikum,_
Na karanta littafinka: *Iyaye ko Miji?* Ya yi kyau ƙwarai, Allaah ya saka da alkhairi. Amma ina da tambaya guda ɗaya: Ana nufin a bayan aure, iyayen mace ba su da sauran haƙƙi a kanta kenan?*AMSA A094*
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._[1] Da farko ya kamata mai tambaya ya san cewa: Dalilin rubuta littafin *Iyaye ko Miji* shi ne: Warware wata matsala da ta daɗe tana ci wa matan aure musulmi a yankinmu tuwo-a- ƙwarya, wadda kuma aka sha raba aure saboda rashin sanin gamsasshiyar amsa a kan ta, ita ce: Wanene ya fi cancantar mace ta yi masa biyayya a lokacin da aka samu saɓani a tsakanin iyayenta da mijinta? Ko kuma a ce: Wanene a tsakanin iyaye ko miji ya fi girman haƙƙi a kan mace? Wannan matsalar ce ɗan ƙaramin littafin ya yi ƙoƙarin warwarewa.
Shiyasa ma a ƙarshensa aka ce:_‘Amma idan miji ya hana matar aikata wani abin da Allaah ya yi umurni, ko kuma ya yi mata umurni da aikata wani abin da Allaah ya hana, bai halatta gare ta ta yi masa biyayya ba a cikin haka, domin Annabi_ _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:_ *‘Babu biyayya ga wani mahaluki a cikin saɓon Mahalicci.’*
Wannan ya nuna ba a cikin kowane abu ne mace take yi wa mijinta biyayya ba.[2] Amma maganar haƙƙoƙin iyaye a kan mace, wannan bai sauka daga kanta ba saboda ta yi aure. Har yanzu wajibi ne ta girmama iyayenta, ta mutunta su, ta gaya musu magana ta darajawa da martabawa, kamar yadda haka ya ke a kan mijinta shi ma dangane da iyayensa. Allaah Ta’aala ya ce:
* ﻭﻗﻀﻰ ﺭﺑﻚ ﺃﻥ ﻻ ﺗﻌﺒﺪﻭﺁ ﺇﻵ ﺇﻳﺎﻩ ، ﻭﺑﺎﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ﺇﺣﺴﺎﻧﺎ ، ﺇﻣﺎ ﻳﺒﻠﻐﻦ ﻋﻨﺪﻙ ﺍﻟﻜﺒﺮ ﺃﺣﺪﻫﻤﺂ ﺃﻭ ﻛﻼﻫﻤﺎ ﻓﻼ ﺗﻘﻞ ﻟﻬﻤﺂ ﺃﻑ ، ﻭﻻ ﺗﻨﻬﺮﻫﻤﺎ ، ﻭﻗﻞ ﻟﻬﻤﺎ ﻗﻮﻻ ﻛﺮﻳﻤﺎ ، ﻭﺍﺧﻔﺾ ﻟﻬﻤﺎ ﺟﻨﺎﺡ ﺍﻟﺬﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﺔ ، ﻭﻗﻞ ﺭﺏ ﺍﺭﺣﻤﻬﻤﺎ ﻛﻤﺎ ﺭﺑﻴﺎﻧﻲ ﺻﻐﻴﺮﺍ *
*Kuma Ubangijinka ya hukunta cewa: Kar ku yi bauta ga kowa sai dai gare shi, kuma iyaye biyu ku kai matuƙa wurin kyautata musu. Idan ɗayansu ku dukkansu biyu ya tsufa a tare da kai, to kar kace musu tir! Ko kash! Ko Haba! Kuma kar ka tsawace su ko ka kaurara ko ka munana musu magana, amma dai ka faɗa musu magana ta mutuntawa da darajawa. Kuma ka tattara su gare ka, kuma ka ƙasƙantar da kai gare su saboda tausayawa. Kuma ka riƙa cewa: Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka rene ni a lokacin ina ƙarami.* _(Surah Al-Israa’i: 23-24)_
A wurin fassara maganarsa: *{Kuma ka tattara su gare ka, kuma ka ƙasƙantar da kai gare su saboda tausayawa},* Urwatu Bn Az-Zubair ya ce:* ﻟَﺎ ﺗَﻤْﺘَﻨِﻊْ ﻣِﻦْ ﺷَﻲْﺀٍ ﺃَﺣَﺒَّﺎﻩُ *
*Kar ka ƙi yin duk wani abin da suke so.* _(At-Tabariy da Ibn Abi-Shaibah; Sahihi ne, in ji mai Rasshul Bard, shafi: 18)_
Wannan ya nuna:(I) Kyautata wa iyaye abu ne da Allaah Ta’aala ya hukunta shi.
(ii) Allaah ya hana a yi wa iyaye duk abin da ke nuna ƙosawa ko gajiya da su.
(iii) Wajibi ne a gaya wa iyaye magana ta girmamawa da darajawa da martabawa.
(iv) Wajibi ne a riƙa tausaya wa iyaye, a nisanci duk abin da ba su so, in dai ba saɓo ba ne.
(v) Wajibi ne a riƙa yi wa iyaye addu’ar Allaah ya rahamshe su.
A wata ayar kuma ya ce:* ﻭﻭﺻﻴﻨﺎ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﺑﻮﺍﻟﺪﻳﻪ ﺣﻤﻠﺘﻪ ﺃﻣﻪ ﻭﻫﻨﺎ ﻋﻠﻰ ﻭﻫﻦ ﻭﻓﺼﺎﻟﻪ ﻓﻲ ﻋﺎﻣﻴﻦ ، ﺃﻥ ﺍﺷﻜﺮﻟﻲ ﻭﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻚ ، ﺇﻟﻲ ﺍﻟﻤﺼﻴﺮ . ﻭﺇﻥ ﺟﺎﻫﺪﺍﻙ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺗﺸﺮﻙ ﺑﻲ ﻣﺎ ﻟﻴﺲ ﻟﻚ ﺑﻪ ﻋﻠﻢ ﻓﻼ ﺗﻄﻌﻬﻤﺎ ، ﻭﺻﺎﺣﺒﻬﻤﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻣﻌﺮﻭﻓﺎ ، ﻭﺍﺗﺒﻊ ﺳﺒﻴﻞ ﻣﻦ ﺃﻧﺎﺏ ﺇﻟﻲ ، ﺛﻢ ﺇﻟﻲ ﻣﺮﺟﻌﻜﻢ ، ﻓﺄﻧﺒﺆﻛﻢ ﺑﻤﺎ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﻌﻤﻠﻮﻥ *
*Kuma mun yi wasiyya ga mutum dangane da iyayensa biyu - mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa rauni a kan rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu - cewa: Ka gode mini, kuma da iyayenka, makoma a gare ni ta ke. Kuma idan suka yi ƙoƙari a kan sai ka yi tarayya da ni a cikin abin da ba ka da iliminsa, to kar ka yi musu biyayya. Amma ka zauna tare da su a duniya cikin kyautatawa, kuma ka bi hanyar wannan da ya mayar da al’amura gare ni, sannan makomarku duk zuwa gare ni ta ke, sai in ba ku labari a kan duk abin da kuka kasance kuna aikatawa.* _(Surah Luqman: 14-15)_
Wannan ya nuna:
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Kısa Hikaye*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: