*HUKUNCIN WANDA YA MANCE ADADIN RAKA'O'IN DA YA YI A SALLAH

298 4 0
                                    

*011 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*HUKUNCIN WANDA YA MANCE ADADIN RAKA'O'IN DA YA YI A SALLAH*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam. Muna godiya sosai da irin qoqarin da kuke yi Allah ya saka maku da mafifichin Alkhairi. Ameen.
Tambayata ita ce: Malam ina sallar Isha'i ina tahiya sai nake ga kamar na yi raka'a uku ne. Malam zan sallame na sake wata sallah ce ko yaya zan yi? Allah ya qara sani mai amfani ameen. Na gode malam.

AMSA:

Wa'alikumus Salam, idan aka sami rafkannuwa a sallah ba sallamewa ake yi a sako daga farko ba, duk yadda sallah ta rikice akwai yadda za a gyara ta, idan an tambayi malamai za su ba da mafita in Allah ya so.

Mutumin da ke yin sallah sai rafkannuwa ta same shi, sai ya yi shakkar adadin raka'o'in da ya sallata, hukuncinsa shi ne zai yi gini ne a kan adadin naqasu, wato misali sallar Isha'i, sai da mutum ya zo tahiya ta qarshe sai ya yi shakkar shin raka'o'i uku ya y i ko huɗu? To a nan sai ya yi wa kansa hukunci a matsayin raka'o'i uku ya yi, sai ya miqe ya kawo ta huɗu, ya yi tahiya ya yi sallama, sai kuma ya yi sujjada biyu bayan sallama, wato sujjar ba'adi.

Haka hukuncin yake a sauran sallolin farillah, matuqar mai sallah ya yi shakkar adadin da ya sallata zai yi gini ne a kan ɓangaren ragi.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
7/4/1440 H.
14/12/2018 M.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now