*Tambaya ta 115*
*ADADIN KWANAKIN JININ HAIHUWA*
_As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah,_
Don Allaah ina son a tambaya mini Malam: Kwana nawa ne adadin kwanakin jinin biƙin haihuwa; domin na ji wani yana cewa wai idan jinin bai tsaya a kwana arba’in (40) ba, za a iya kai wa har kwanaki sittin (60). Ina son ƙarin bayani, _please_ .
*AMSA A115:*
_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh._
[1] Al-Imaam Abu-Daawud da Al-Imaam At-Tirmiziy da Al-Imaam Ibn Maajah duk sun riwaito hadisin da Al-Imaam Al-Muhaddith Al-Albaaniy ya _hassana_ shi a cikin *Al-Irwaa’u (lamba: 201),* daga Sahabiya Ummul-Mu’mineen Ummu-Salamah _(Radiyal Laahu Anhaa)_ cewa:
A zamanin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ita mai jinin haihuwa tana zama a cikin jininta har zuwa kwanaki arba’in ne. Kuma ba ya umurtan ta da rama sallolin da ba ta yi su a halin tana jinin haihuwar ba.
[2] Al-Imaam Abu-Isaa At-Tirmiziy a ƙarshen riwayarsa ga wannan hadisin ya ce:
‘Malamai ma’abuta ilimi daga cikin Sahabban Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ da Tabi’ai da waɗanda suka bi bayansu duk sun haɗu a kan cewa: Ita mai jinin haihuwa tana barin yin sallah na tsawon kwanaki arba’in ne, sai dai ko in ta ga tsarki kafin hakan. Daga nan sai ta yi wanka ta cigaba da sallah.
Idan kuma ta ga jinin a bayan kwanaki arba’in ɗin ne, to mafi-yawan malamai masana ilimi sun ce, ba za ta bar yin sallah a bayan kwana arba’in ba.
Wannan kuma shi ne maganar mafi-yawa daga cikin malaman Fiqhu, shi ne maganar Sufyaan At-Thawriy, da Ibn Al-Mubaarak, da As-Shaafi’iy, da Ahmad, da Is’haaq.’
[3] Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah _(Rahimahul Laah)_ ya ce:
‘Jinin haihuwa ba shi da iyaka ta fuskar ƙaranci ko ta fuskar yawa. Don haka, idan aka ƙaddara cewa wata mace ta ga zuban jinin fiye da kawanaki arba’in ko sittin ko saba’in kuma a yanyanke, to dai jinin haihuwa ne.
Amma idan a haɗe da juna ne, to shi jinin istihaalah ne, kuma a lokacin sai a ce: Bakin iyakan kwanakinsa arba’in ne, domin shi ne iyakan kwanakin yawancin mata, kamar yadda hadisi ya nuna.’ _(Tamaamul Minnah: 1/144)._
[4] Ibn Qudaamah Al-Maqdisiy a cikin littafinsa *Al-Mughnee: 1/392* ya ce:
‘Idan jinin haihuwa ya zarce kwanaki arba’in sai kuma ya dace da lokacin al’ada, to shi haila ne. Idan kuwa bai dace ba, to shi *Istihaalah* ne.’
[5] Game da matar da ta tsarkaka daga jinin haihuwa kafin kwana arba’in, daga baya kuma sai jinin ya dawo mata kafin cikan kwanaki arba’in ɗin, shi ne Al-Allaamah Ibn Al-Uthaimeen _(Rahimahul Laah)_ a cikin *As-Sharh Al-Mumti’: 1/450* ya ce:
‘Sai ta lura da alamomin jinin: Idan ta ga siffofin jinin haihuwa a tare da shi, to jinin haihuwa ne.
Idan kuwa alamun ba su nuna shi jinin haihuwa ba ne, to ita mai tsarki ce. Kuma Allaah shi ne Masani.’
[6] Al-Imaam Al-Muhaddith Al-Albaaniy _(Rahimahul Laah)_ kuma ya ce:
‘Mace tana zama har kwana arba’in ne a matsayin mai jinin haihuwa. Idan kuma jinin ya yi ta-zarce a bayan haka, to sai a ba ta hukuncin mai *Istihaadah.’* _(Al-Mausuu’ah: 1/269)._
_Wal Laahu A’lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
22/7/2019
10: 25pm.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: