*HUKUNCIN MATAR DA KE QAURACE WA MIJINTA A SHIMFIDA

107 1 0
                                    

*203 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*HUKUNCIN MATAR DA KE QAURACE WA MIJINTA A SHIMFIDA?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum dan Allah mallam laifi ne dan mijin mace ya bata mata rai ta yi yaji ta qaurace masa a wajen shimfida?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, ƴar uwa a gaskiya abin da Shari'a ta nuna shi ne bai halasta mace ta qaurace wa mijinta a shimfiɗa ba ko da ya ɓata mata rai matuqar ya kiyaye haqqoqinta da Allah ya wajabta masa, saboda hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah Allah ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce:
"Idan namiji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa sai ta qi, har ya kwana yana fushi da ita, to Mala'iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari".
Bukhariy 3237, Muslim 1436.

Saboda haka lallai mata su guji qaurace wa mazajensu a lokacin da suka buqace su, saboda kauce ma wannan tsinuwa na Mala'iku, su kuma mazaje su ji tsoron Allah su daina quntata wa matayensu.

Abubuwan da suke zama uzuri ga macen da mijinta ya neme ta ta qi su ne, kamar mace tana jinin haila, ko jinin biqi, ko rashin lafiyar da idan ta yi jima'i za ta cutu, ko abin da ya yi kama da haka na uzuri karɓaɓɓe a Shari'a, sai dai shi jinin haila da na biqi ɗin suna hana saduwa ne, amma ba sa hana jin daɗi daga abin da ke saman gyauto.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
6/12/1440 h.
07/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now