*022 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*WACCE ADDU’A AKE KARANTAWA IDAN HAILA TA ZO?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Malam da fatan kuna lafiya Allah ya saka muku da alkairi, dan Allah ina da tambaya, tambayar ita ce shin akwai addu’a da mace take yi yayin da jinin al'ada ta zo mata wadda ta fara da alhamdu lillahi ala kulli halin? Dan Allah a taimaka min da ita, na gode.
AMSA:
Wannan ba shi da asali a addini, duk hukunce-hukuncen jinin haila da malamai suka yi magana a kai, da wahala mutum ya sami bayanin wannan addu'ar a ciki, don haka wannan addu'a da ake yi a lokacin da haila ta zo wa mace ba shi da asali a addini.
Abin da mace ya kamata ta ba muhimmanci a lokacin da jinin haila ya zo mata shi ne abubuwan da Shari'a ta ce mai jinin haila ta yi, kamar dakatar da jima'i da miji idan ta kasance matar aure ce, da sanya abin da zai riqa tare jinin yana tsane shi (ƙunzugu ko pad), da canja shi qunzugun a kan lokacin da ya dace, da dakatar da yin sallah da azumi, da sauran su, har zuwa lokacin ɗaukewar jinin.
Allah ne mafi sani.*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
23/4/1440 h.
30/12/2018 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: