*WANKAN TSARKI DA KITSO NA ULU

302 0 0
                                    

*Tambaya ta 010:*

*WANKAN TSARKI DA KITSO NA ULU*

_Assalamu Alaikum._

Malam don Allaah, ina da tambaya.

Wai kitson zare na ulu wanda aka yi ƙari yana wankan tsarki?

*AMSA A010:*

_W alkm slm w rhmt laah._

1. A cikin Hadisin Abu-Hurairah _(Radiyal Laahu Anhu)_ wanda Al-Imaam Muslim _(Rahimahul Laah)_ ya fitar da shi, Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi bayanin siffofin waɗansu mata 'yan wuta daga cikin al'ummarsa, waɗanda kuma ko ƙanshin Aljannah ma ba za su ji ba, balle ma su shiga cikinta. Ya ce:

*وَنِسَاءٌ كَاسِيَاتٌ عَارِيَاتٌ ، مَائِلَاتٌ مُمِيلَاتٌ ، رُؤُوسُهُنَّ كَأَسْنِمَةِ الْبُخْتِ الْمَائِلَةِ*
*Da waɗansu mata masu sanye da tufafi amma kuma suna tsirara! Karkatattu, masu karkatarwa! Kawunansu kamar tozayen raƙumma karkatattu!*

2. A wurin sharhi da ƙarin bayani a kan siffar ' *kawunansu kamar tozayen raƙumma'* sai malamai irinsu Al-Imaam An-Nawawiy _(Rahimahul Laah)_ suka ce:

Suna girmama girman kawunan nasu ne ta hanyar nannaɗa manyan rawunna, ko cukwikwiya tsummokara da makamantansu a kawunan nasu, har sai sun yi kamar tozayen raƙumma!

3. Daga nan muke fahimtar cewa:

Matsalar yin kitso, ko yin ‘ _attachment’_ da zaren ulu ba ƙaramar matsala ba ce. Domin tana da alaƙa mai ƙarfi wurin hana mai yinsa samun kusanta, balle ma shiga Gidan Aljannah a Lahira!

4. Don haka, mas'alar ta fi ƙarfin maganar halacci ko rashin halaccin yin wankan tsarki da shi. Haka kuma maganar ta wuce batun irin abin da aka maƙala a cikin gashin: Ko ulu ne, ko gashin mutum ne, ko na dabba, ko na tsuntsu, ko kuma tsumma ne kawai, da sauransu!

5. Amma game da wankan tsarki, a zance mafi inganci a wurin malamai: Akwai babbar matsala, idan aka ƙyale mai _‘attachment’_ ta cigaba da yin wankan tsarki da su a kanta.
Domin tun da dai ana umurtan wacce ba ta sanya irin wannan abin a kanta ba da ta warware kitson gashin kanta a wurin wankan haila (ban da na janaba), a zance mafi ƙarfi a wurin malamai, wannan ya nuna lallai ita ma da ta yi wannan ƙarin a kanta, lallai sai ta warware shi, a wurin wankan tsarki (haila ko nifasi).

_Wal Laahu A'lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
30 - 1 - 2018

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now