*MENE KALMAR NASIHATUL LILLAHI DA TA ZO A HADISI TAKE NUFI?*

107 0 0
                                    

*007 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*MENE KALMAR NASIHATUL LILLAHI DA TA ZO A HADISI TAKE NUFI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Me a ke nufi da nasihatullillah? Na gode Allah ya qara basira.

AMSA:

Wato wannan lafazi na "Nasihatullillahi" ya zo a hadisi na bakwai da ke cikin littafin الأربعون النووية (Arba'una Hadis), inda Annabi s.a.w yake cewa:
"Addini Nahiha ce, sai Sahabbai suka ce; nasiha ga wane? Sai Annabi s.a.w ya ce masu, Nasiha ce ga Allah da littafin Allah, da Manzon Allah, da shugabannin Musulmai, da kuma gama'garin Musulmai". Wato addini Nasiha ce ga waɗannan ɓangarori guda biyar.

Sheikh Ibn Uthaimeen a cikin sharhin da ya yi wa wannan hadisin, a littafinsa na sharhin Arba'una Hadis ya bayyana cewa; abin da ake nufi da NASIHATULLLILAHI shi ne abubuwa guda biyu kamar haka:

١. إخلاص العبادة له.

Wato na farko yana nufin: Tsarkake bauta a gare shi (Allah).

٢. الشهادة له بالوحدانية في ربوبيته وألوهيته وأسمائه وصفّاته.

Na biyun nan kuma yana nufin: Shaidar masa da kaɗaituwa a abubuwan da ya halitta, da cancantar bauta a gare shi shi kaɗai, da kaɗaita shi a sunayensa, da siffofinsa. Allama Ibn Uthaimeen ya ce, waɗannan abubuwa biyu su ne abin da NASIHATULLILLAHI (Nasiha ga Allah) yake nufi.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
3/4/1440 H.
10/12/2018 M.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now