*LIKITA DA CIN KUDIN SCAN*

187 0 0
                                    

*TAMBAYA TA 105*

*LIKITA DA CIN KUDIN SCAN*

_As-Salaamu Alaikum,_

Likitan da yake duba mutane a asibiti sai kuma ya aika su wani wurin don yin _scaning_ da yin gwaji, daga baya kuma sai masu wurin scan ɗin su aiko masa da ribarsa a ƙarshen wata. Yaya matsayin wannan kuɗin da Likitan ke kar6a?

*AMSA A105*

_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._

Da farko abin da ya dace a fara sani a nan shi ne:

Shin likitan yana aiki a ƙarƙashin wani asibitin gwamnati ne ko wata cibiyar lafiya mai zaman kanta, ko kuwa a wani asibitin da shi kansa ya buɗe ne?

Idan ba a asibitinsa ba ne, shin ko asibitin da yake aiki a cikinsa yana da nasa wurin gwaje-gwajen kuma yana aiki yadda ya dace, ko kuma dai ba shi da shi?

Idan babu, shin ko masu asibitin da yake aiki a cikinsa sun iyakance masa cewa, ya riƙa aikawa da marasa lafiya zuwa wannan wurin binciken ne kawai, ko kuwa yana da daman ya za6i duk wurin da ya ga dama?

Idan sun iyakance masa ko ba su iyakance masa ba, to ko sun san da wannan yarjejeniyar ta kuɗi a tsakaninsa da wurin yin gwaje-gwajen, ko ba su sani ba?

Idan sun sani, shin ko sun yarda ya riƙa zuba abin da suka kawo a cikin aljihunsa ne, ko kuwa a cikin asusun asibitin ne?

Idan ba su sani ba, ko kuma idan sun sani amma ba su yarda ya kar6a ko ya zuba a aljihunsa ba, to a nan sai a janyo masa hadisi Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ mai cewa: *Duk wanda muka ɗauke shi aiki kuma muka yanka masa albashi, to duk abin da ya ci a bayan hakan ya ci haram!*  _(Sahih Al-Jaami’u: 6023)._

Amma idan asibitinsa ne, kuma shi da kansa ne ya yi yarjejeniya da wurin yin gwajin, to a nan ba abin da za a ce, sai dai a janyo hadisin da ya ce: *Musulmi suna nan a kan sharuɗɗansu, sai dai sharaɗin da ya haramta halal ko ya halalta haram.* _(Sahih Al-Jaami’u: 6714-6716)_

Wannan shi ne abin da zan faɗa.

_Wal Laahu A’lam._

*sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
19/06/2019

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now