*TAMBAYA TA 020*
*AUREN MAI CIKIN-SHEGE DON RUFA MATA ASIRI*
_Assalamu Alaikum._
Malam, wata ce ta yi cikin-shege da wani mutum, sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri, ya aure ta. Yanzu haka dai sun yi auren. Yaya hukuncin auren ya ke a Shari’a?
*AMSA A020:*
_W alkm slm w rhmtul Laah._
[1] Ma’anar cikin-shege shi ne: Ta samu cikin ta hanyar zina, ko ‘saduwa’ da wanda ba mijin da aka ɗaura musu sahihin aure ba.
Kowa kuwa ya san cewa wannan mummunan haram ne a cikin koyarwar addinin musulunci.
Allaah Ta'aala ya ce:*وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَى ، إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَآءَ سَبِيلاً*
*Kuma kar ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce.*[2] Sannan wannan ɗan da aka samu ta wannan hanyar ba za a jingina shi ga wanda ya yi mata cikin ba, a shari’ance. Don haka, ko da ɗayansu ya mutu babu gado a tsakaninsu. Haka kuma babu duk wata dangantaka da ta ke tsakanin Uba da ɗa.
[3] Hukuncin da Shari’ar Musulunci Mai Adalci ta yanke musu shi ne: Idan ba su riga sun yi aure ba a lokacin da suka aikata laifin, sai a yi wa kowane ɗaya daga cikinsu buloli guda ɗari a gaban jama’ar musulmi, ba tare da nuna wani tausayi gare su ba, tare da ɗaurin shekarar guda, kamar yadda ya ambata a cikin *Suratun Nuur* .
Idan kuwa dukkansu ko ɗayansu ya taɓa yin aure, to bayan bulolin sai a ƙara masa da jefewa da duwatsu har sai ya mutu, kamar yadda Sunnah Sahihiya ta nuna.
[4] Amma game da maganar aurenta da wanda suka yi zinar da shi, ko da wani musulmi, wannan ba zai yiwu ba sai bayan ta cika waɗansu sharuɗɗa, kamar haka:
(1) Sai ta tuba tuba ta gaskiya a bisa sharuɗɗan da Malamai suka shimfiɗa, tun kafin mahukunta su samu iko a kanta, ko kuma bayan an gama yi mata haddin. Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:
*الزَّانِي لَا يَنْكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً ، وَالزَّانِيَةُ لَا يَنْكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ ، وَحُرِّمَ ذَلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ*
*Mazinaci ba ya yin aure sai da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya ba mai aurenta sai mazinaci ko mushiriki, kuma an haramta wannan ga muminai* .(2) Sai ta yi *istibra’i* , watau ta zauna na tsawon lokacin da za a tabbatar cewa babu jariri a cikin mahaifarta. Watau sai ta yi ko da haila guda.
Amma a nan, tun da an tabbatar da cewa tana da ciki, to ba zai yiwu a ɗaura auren ba sai bayan ta haihu, saboda maganar Allaah Ta’aala cewa:
*وَأَوْلَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَّضَعْنَ حَمْلَهُنَّ*
*Kuma masu cikunna iddarsu ita ce su haife cikinsu.*Don haka, in dai har da gaske ne cewa wannan matar ta yi cikin-shege, kuma ta yi aure da wani don ya rufa mata asiri, to ba shakka an yi haram, wannan auren bai halatta ba. Kuma dole ne a raba su, ta koma ta zauna har sai ta haife cikin nata tukun.
_Wal Laahu A’lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
20-2-2018
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: