*HUKUNCIN AURAN KASHE WUTA*
*TAMBAYA*
Menene hukuncin wanda ya auri wata dan ya saketa dan ta koma gidan mijinta nada batare da mijinta ya sani ba?*AMSA*
Wa'alaikumussalam Warahmatullahi Wabarakatuhu, irin wannan auran ya kasu gida biyu:
(1)Wanda aka yi shi da sharadi, misali mutum da mace da mijinta da ya sake ta, suyi ittifaki akan shi wannan mutumin zai aure ta amma da sharadin zai sake ta domin ta komawa mijin ta na farko wannan mallamai sunyi ittifaki a kan haramcin shi kuma auran bai inganta ba wato lalataccene.Shi yasa Manzon Allah (SAW) Ya ce: "لعن الله المحلل والمحلل له"Abu Dawud hadisi na (2078) da Ibnu mãjah Hadisi na (2011).
(2)Nau'i na biyu shine wanda akayi shi bada sharadiba,misali wanda ya auri mace sai ya sake ta domin ta halasta ga mijin ta na farko da ya sake ta, irin wannan Imamu Shafi'i da riwaya daga Abu Hanifa suna ganin yanada laifi amma auran da yayi ingantacce ne, sannan an ruwaito wannan daga Urwatu bin Zubair da Salim bin Abdullahi da Qasim bin Muhammad da Imamu Sha'abi da sauransu.
Suna ganin fadin Manzon Allah( SAW) لعن الله المحلل والمحلل له Baya nuna cewa auran ba ingantacce bane sai dai wadanda suka yishi suna da zunubi.
*Amma abinda ya fi inganci wanda mallamai suka tafi a kai kamar yadda Shaikhul Islam 'Ibnu Taimiyya ya fada kuma shine Ijmaa'in sahabban Manzon Allah(SAW) dukkan nau'o'in guda biyu haramun ne.والله تعالى أعلم
Domin neman karin bayani a duba littattafan nan:
١/سنن أبي داود،رقم الحديث (٢٠٧٨)،ج٦،ص:(٦٦).
٢/سنن ابن ماجة،رقم الحديث:(٢٠١١ )،ج٦،ص:(١٤٤).
٣/نيل الأوطار للشوكاني،ج٦،ص:(١٦٥).
٤/الفتاوى الكبرى لابن تيمية،ج٦،ص:(٨).
٥/المستدرك على مجموع الفتاوى،ج٤،ص:(١٧٤).03/05/2019
*DR NASIR YAHYA ABUBAKAR B/GWARI*
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Krótkie Opowiadania*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: