*HUKUNCIN SAQONNIN DA AKE CEWA WANDA BAI TURA BA ZAI HADU DA BALA'I

136 3 0
                                    

*042 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*HUKUNCIN SAQONNIN DA AKE CEWA WANDA BAI TURA BA ZAI HADU DA BALA'I*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Don Allah malam mene ne hukuncin saqon da za a turo ana faɗin cewa an yi mafarki cewan duk wanda ya tura zai kasance cikin alkhairai masu yawa, wanda kuma bai tura ba bala'i da musiba za su afku mishi?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam. A gaskiya Ire-iren waɗannan saqonni da a qarshensu ake cewa idan ka tura wa adadin mutane kaza za ka ga abin alheri, idan kuma ka qi tura ma kowa za ka haɗu da bala'i da musiba nan da kwana kaza, duk irin waɗannan maganganu qarya ce kawai tsabarta, domin ko addini ba a ce dole ne sai an tilasta mutum ya yi ba, balle kuma tura wani saqon da ba shi da asali.

Sau da yawa masu qirqirar ire-iren waɗannan saqonnin suna jingina qarya ga limamin Makka ko Madina ne, ko su jingina qarya ga mai gadin masallacin Annabi s.a.w, su ce wai limamin Makka ko na Madina ko mai gadin masallatan ya yi mafarkin Manzon Allah s.a.w ya ce masa kaza da kaza, kuma Annabi ya umarce shi ya isar wa da mutane wannan saqo, kuma duk wanda ya ji ko ya ga wannan saqo idan bai isar wa da adadin mutane kaza ba, to bala'i da musiba za su same shi nan da kwana kaza, idan kuma mutum ya isar wa da adadin mutane kaza ko kaza zai ga alheri a rayuwarsa.

Wani lokacin ma har da rantsuwa suke haɗa wa su ce wai wani mutum a wani gari ko wata qasa ya ga wannan saqo ya tura wa adadin mutane kaza sai ya sami alheri mai yawa a rayuwarsa, wani kuma ya ga saqon sai ya qi tura ma kowa sai Allah ya mayar da shi biri, ko kare, ko su ce wai ya sami karayar arziki saboda qin tura ma kowa.

A gaskiya duk irin waɗannan saqonni qarya ce tsantsa suke jingina ma waɗancan limamai ko masu gadin Haramain, kuma qarya ce tsantsa suke wa Annabi s.a.w. Kuma Annabi s.a.w ya ce: "Duk wanda ya jingina mini qarya da gangan ya jiraci masaukinsa a wuta".
Bukhariy 1291. Muslim 3004.

Addini ya riga ya cika, babu wani alheri da Annabi s.a.w ya bar shi bai nuna ma al’ummarsa ba, haka kuma ba wani sharri da bai faɗakar da mu shi ba. Don haka mu guji yi wa Annabi s.a.w qarya da yaɗa qaryar da aka yi masa, Allah ya kare mu da yi wa Annabi s.a.w qarya, amin.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
21/5/1440 h.
27/01/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now