TAMBAYA TA 095
ƁATA WA KISHIYA MU’AMALAR AURE
As-Salamu Alaikum,
Malam, mu uku ne a wurin mijinmu. Shi yana zaune a Abuja tare da ɗaya, ni kuma da ɗayar muna zaune a gari daban-daban. A kullum da safe da yamma sai ya kira ’yar uwar zamana sun gaisa. Haka ma a lokacin da muka zo kwanciya, sai ya kira ta sun taɓa soyayya sannan ya fuskance ni. shiyasa abin yake fita a kaina. Wai shin ina da haƙƙi ni ma ya riƙa kira na kullum? Kuma menene hukuncin ɓata mana mu’amalar auratayya da suke yi? Allaah ya ba da ikon amsawa.
AMSA A095Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
[1] Da farko dai dole duk mu san cewa: Adalci a tsakanin kishiyoyi a cikin abubuwan da su ke a bayyane wajibi ne, kuma zalunci ko cuta a tsakaninsu haram ne. Domin idan miji bai iya yin adalci a tsakanin matansa a cikin irin waɗannan abubuwan na fili ba, to yana da alƙawarin za a yi masa matsanancin azaba a Lahira.
A ƙarƙashin wannan dole ne miji ya daidaita kwanansa a wurin kowacce daga cikin matansa, da ta-kusa da ta-nesa: Ko dai ta hanyar zuwa ya same ta a inda ta ke, ko kuma ta hanyar kiranta ta zo inda ya ke. Haka kuma sauran abubuwan da suke a fili kamar rabon abinci da abin sha da bayar da kyauta da makamantansu. Sai fa ko in ita matar ce da kanta ne ta amince ta kayar da haƙƙinta a kan wani sulhu ko yarjejeniya a tsakaninsu. Muhimmin abu dai dole ne miji ya kasance bai cuci kowacce mace daga cikin matansa ba. An bayyana irin haka a cikin amsoshin da suka gabata kamar tambaya ta A065 da A081.
Amma ko za a sanya kiran waya a cikin waɗannan abubuwan da aka ɗora wa miji tilas ya daidaita a tsakanin matansa a kansu, ko kuwa shi yana cikin abubuwan da buƙata ce ke tayar da su, waɗanda kuma ba a ɗora wa miji daidaita wa a cikinsu ba, kamar: Murmushi da dariya da ƙauna da sha’awar saduwa da sauransu? Amsar wannan za ta bayyana ne idan aka san abin da ya haifar da kiran wayar a tsakaninsu. Idan ya kasance wata larura ce karɓaɓɓiya a shari’a ta ke sanya su yin waya a wannan lokacin, shikenan. Amma idan ya kasance shegantaka ce kawai, don neman a muzguna ko ɓata wa abokiyar zama rai, to wannan kuma a fili ya ke cewa zalunci ne da dole sai an rama wa wadda ake cuta, ko kuma a nemi yafewarta.
[2] Amma ke ma kuma dole a tambaye ki: Shin kin iya, kuma kina taɓa ’yar soyayyar ke ma a tsakaninki da shi? Domin da yawa mace takan yi sakaci a wannan fannin har wata macen ta kwace mata miji. Wata saboda sakaci a kan tsafta ko kwalliya ko gyara abinci ko tarairaya da janyo hankalinsa gare ta, da sauransu. Idan mace ba ta iya ba, ko kuma idan ta ƙi yin waɗannan ’yan abubuwan yadda ya dace, daidai yadda ya dace, kuma a daidai lokacin da ya dace, dole ne ta samu matsaloli a gidan aurenta, ba wai matsala kaɗai ba. Shiyasa tun a shekarun baya manyan malamai suka yi wa’azozi a kan haka, kamar: Bi ta zai-zai na Mal. Ja’afar da Sihirul-Halaal na Mal. Albaaniy, Allaah ya ji ƙansu.
[3] Sannan kuma ko kin taɓa bayyana ma mijinki damuwarki a kan haka? Wace amsa ya ba ki? Kuma shin ko ke ma kin taɓa gwada kiransa a lokacin yana wurin waccan a irin waɗannan lokutan? Me ya biyo bayan hakan?
Daga amsoshin waɗannan tambayoyin ne za ki iya fahimtar abubuwa daga gare shi, har kuma ki san irin matakan da suka kamata ki ɗauka domin warware matsalar ke da kanki.Allaah ya shiryar da mu gaba-ɗaya ga abin da yake so kum yake yarda da shi.
Wal Laahu A’lam.
25/5/2019
10: 31pm*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafy*
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: