WANDA YAKE ZUWA WALIMA BA'A GAYYACE SHI BA, BA ZA'A AMSHI SHAIDARSA BA !

178 4 0
                                    

*WANDA YAKE ZUWA WALIMA BA'A GAYYACE SHI BA,  BA ZA'A AMSHI SHAIDARSA BA !*

*Tambaya*

Assalamu Alaikum malam, meye ingancin hadisin dake cewa babu sallah ga makobcin masallaci sai Acikin masallaci.
Haka kuma ko akwai hadisi tabbatacce dake nuni da haramcin cin abincin walima ga Wanda ba a gayyataba? Allah bawa malam ikon ansa tambayar. Ina maka fatan Alkairin dunia da lahira

*Amsa*

Wa'alaikumus Salam
Hadisin babu Sallah ga makocin masallaci sai a Masallaci bai inganta ba, saidai ya inganta a matsayin maganar Aliyu Bn Abi-dalib. .

Ibnu Khudhamah ya yi bayani cewa: Ba'a amsar shaidar wanda yake zuwa walima ba'a gayyace shi ba, Al-mugni 12/50.
Akwai hadisin Bukhari Wanda yake nuna karhancin cin abincin walima ga wanda ba'a gayyata ba,  saboda lokacin da wani ya biyo Manzon Allah wajan cin abincin da ba'a gayyace shi ba, saida ya nemi iznin mai gayyatar, Sannan mutumin ya shiga. Bukhari (1975)

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

20/07/2019

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now