*Tambaya ta 004:*
*GANIN TSIRAICIN ’YA MARA LAFIYA*_Assalamu Alaikum_ .
Tambayata ita ce, watau ina da 'ya wadda ba ta da lafiya, tun tana shekara 6 ta fara rashin lafiya, yanzu kuma shekarunta 27. Ni ce nake mata komai.
Fatawar da nake nema a nan ita ce, yarinyar ba ta da cikakken hankali sosai, domin kusan dai ba komai take sani a kan menene yake faruwa a rayuwar duniya ba, farfaɗiya take da shi. _‘So’_ dole ne nake ganin tsiraicinta, domin ni ce nake mata dukkan hidimarta, _‘so’_ nakan yawan yin tunani haramcin gani tsiraici. Sannan wani lokaci nakan samu kaina a rashin yi mata wanka na gama al’ada.‘ _Please’_ a taimakeni a ba ni wannan fatawar a yi bayaninta.
*AMSA A004:*
_W alkm slm w rhmt Laah._
1. Wataƙila, abin da ya sa kike jin nauyin gani ko kallon tsiraicinta shi ne hanin da addini da al'ada suka yi a kan duban tsiraicin, kamar a cikin Suratun Nur:
*وَقُلْ لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنّ*
*Kuma ka gaya wa muminai mata cewa, su kiyaye ganinsu kuma suka tsare al'aurorinsu.*Saboda wannan ayar ce, malamai suka tabbatar cewa: Duk yayin da yaro ya kai lokacin balaga, to bai halatta mahaifi ko mahaifiyarsa su kalli al'aurarsa ba.
2. Amma a nan, Larura ce za ta buɗe wannan ƙofar da aka rufe. Ma'ana: A nan ƙa'idar nan ta malaman *Usuulil-Fiqhi* za a jawo, mai cewa:
الضَّرُورَاتُ تُبِيحُ الْمَحْذُورَاتِ
Larurori suna halatta abubuwan da aka yi tsawa a kansu.3. Kasantuwar wannan yarinya tana da larura, ta yadda ba ta iya yin komai da kanta, wannan ya sa dole wani ya taimaka ya yi mata abubuwan da suka shafi ba ta abinci, tsarkake jikinta, da yi mata wanka na tsafta da na al'ada, da shafa mata mai, da sanya mata tufafi, da sauransu.
4. Kuma a duk duniya babu wanda ya cancanci yin hakan gare ta sai ke mahaifiyarta. Idan ba kya nan ne sai a nemo 'yarta, ko 'yar uwarta, kafin a waiwayi mahaifi, ko ɗa, ko ɗan'uwanta.
Shiyasa malamai suka amince cewa: Idan aka tsallake miji, to babu wanda ya fi cancantar ya karɓi haihuwar mace in ba mahaifiyarta ba. Amma larura ce ke sanyawa a kai haihuwa wurin wadda ko wanda ba mahaifiyar mace mai juna-biyu ba.
5. A taƙaice dai 'yar uwa, ba ki da wani laifi don kin ga, ko kin kalli tsiraicin 'yarki mai fama da wannan irin larurar. Domin a tsakanin uwa da 'ya babu tsoron aukuwar irin matsalar da kallon tsiraici ke haifarwa a tsakanin sauran jama'a.
Allaah ya kyauta, kuma ya ba ta lafiya. Ya sa wannan larurar ta zama sanadiyyar samun Gidan Aljannah garemu baki-ɗaya.
Allaah ya ƙara miki juriya da ƙarfin-gwiwar tsayawa a kan wannan aikin na alkhairi.
Allaah ya saka da alkhairi.
_Wal Laahu A'lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafy*
28 - 12 - 2017
![](https://img.wattpad.com/cover/186935965-288-k193559.jpg)
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: