*200 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*TSAKANIN UWARGIDA DA AMARYA WACE CE SHUGABA?*
TAMBAYA:
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته.
Malam don Allah meye hukuncin mijin da ya ce wa matarsa dole sai ta bi kishiyoyinta kuma ita ce uwargida?AMSA:
وعليكم السلام ورحمة الله وبركاته.
Magana ta gaskiya a qa'idar rayuwa ta ma'abota hankula qarami ne ke bin babba, duk lokacin da aka ce ga babba sannan kuma ga qarami, to a nan babba shi ne shugaba, kuma shi ya kamata a bi, sai dai idan ya zamo babban ya yar da girmansa, ya zama babba a suna, ba ya aiki da halin manya, to a nan ko da na qasa sun raina shi laifinsa ne, saboda matuqar babba ba ya ba naqasa da shi haqqinsa, to da wahala bai rasa qimar wannan girman tasa ba.Saboda haka, asali amare su ne suka kamata su bi uwargida, amma idan mijin nan naki yana nufin ki zauna da su lafiya ne, ba yana nufin babba ne zai bi qarami ba, to wannan ba matsala ba ce don ya faɗi hakan, idan kuma manufarsa qasqantar da babba, da mayar da qarami babba, to ya yi kuskure, sai a nuna masa ta lalama.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
5/12/1440 h.
06/08/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: