*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN YIN ALLURA YANA KARYA AZUMI?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum, malam don Allah yin allura yana karya azumi idan mutum bai ji shi ta makogwaron shi ba?
AMSA:
Wa'alaikumus salam, yin allura ba ya karya azumi a zance mafi inganci, sai dai fa idan ya zamo allurar abinci ne, wanda idan aka yi shi zai je uwar hanji ya samar da qoshi, amma matuqar allura ba ta abinci ba ce babu laifi idan aka yi ta da azumi, kamar yadda malamai suka tabbatar. Amma idan da za a bari sai bayan shan ruwa da daddare sannan a yi allura, to hakan ya fi kyau.
Sannan kuma allura ba a lissafa ta a cikin jinsin ci ko sha, ko cikin abin da ake kira abinci ko abin sha, hakan sai yake qara nuna cewa yin ta ba ya karya azumi matuqar ba wadda take sa qoshi ba ne.
Duba Fataáwál Lajnatid Daá'ima 10/252. Ko Majmu'u Fataáwá na Sheikh Ibn Bazz 15/257.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
8/Ramadan/1440 h.
13/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: