*TAMBAYA TA 026*
*ƘAYYADE HAIHUWA*
_As Salaamu Alaikum_
Miji ne ba ya bai wa matarsa haƙƙinta na zamantakewa, kamar sakin fuska da hira da bayar da abinci da ɗinka sutura da sauran kayan masarufi irin yadda yake bai wa kishiyarta, wai dole sai ta amince da abin da yake so, wai sai ta yarda a riƙa yi mata allurar rage haihuwa! Meye hukuncin wannan a shari’a?
*AMSA A026:*
_W alkm slm w rhmtul Laah._
[1] Da farko ya kamata duk mu san cewa: Haihuwa baiwa ce kuma kyauta ce daga Allaah Mabuwayin Sarki, yana bayar da ita ga wanda yake so, a sadda, da inda, kuma ta yadda yake so, kamar yadda ya faɗa a cikin *Suratu Shuura:*
لِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَخْلُقُ مَا يَشَآءُ ، يَهَبُ لِمَنْ يَشَآءُ إِنَاثًا وَيَهَبُ لِمَنْ يَشَآءُ الذُّكُورَ ، أَوْ يُزَوِّجُهُمْ ذُكْرَانًا وَإِنَاثًا ، وَيَجْعَلُ مَنْ يَشَآءُ عَقِيمًا ، إِنَّهُ عَلِيمٌ قَدِير
Mulkin sammai da ƙasa na Allaah ne kaɗai, yana halitta duk abin da ya ga dama, yana yin baiwar ’ya’ya mata ga wanda ya ga dama, kuma yana yin baiwar ’ya’ya maza ga wanda ya ga dama, ko kuma ya gauraya su maza da mata (ga wanda ya ga dama), kuma yana ƙyale wanda ya ga dama a matsayin bakarare, haƙiƙa shi mai ɗimbin sani ne, mai cikakken iko.A yau kuwa muna ji da ganin yadda ma’aurata da yawa suke neman haihuwar maza da mata a haɗe, ko irin nau’in da bai ba su ba amma kuma ba su samu ba, kamar kuma yadda muka sha ji da ganin waɗanda suke ta ƙoƙari rani da damina, ba-dare ba-rana don samun ko da haihuwar sau ɗaya ma, amma dayake Mai Yin Baiwar bai bayar ba, dole suka yi haƙuri suka dangana. Sannan kuma a kullum mana ji da ganin yadda ma’aurata suke murna da farin ciki a duk lokacin da Mabuwayin Sarki Mai Yawan Baiwa ya albarkace su da samun haihuwa. Waɗannan abubuwa ne sanannu tabbatattu a cikin musulmi da kafirai da dukkan al’ummomin duniya.
[2] Ni’imomin da Ubangiji Ta’aala ya yi wa bayinsa a koyaushe suna da yawan gaske, kamar yadda ya faɗa a cikin *Suratun Nahl:*
وَإِنْ تَعُدُّوا نِعْمَةَ اللَّهِ لَا تُحْصُوهَا إِنَّ اللَّهَ لَغَفُورٌ رَحِيمٌ
Kuma in da za ku lissafe ni’imomin Allaah a gare ku, ba za ku iya ƙididdige su ba, lallai Allaah tabbas! Mai Yawan Gafara ne, Mai Yawan Rahama ne.Sai dai kuma duk da hakan ba mu taɓa ko jin labarin wani mutum guda ɗaya mai hankali da tunani ba ya taɓa ƙyamatar ko da mafi ƙanƙantar baiwa guda daga cikin ɗimbin ni’imomin Ubangiji Ta’aala ba a gare shi. Babu wanda ya taɓa ƙyama ko jin haushi idan itatuwan mangwaro ko lemu ko ayaba a gonarsa suka fitar da ’ya’ya masu yawan da bai taɓa ganin irinsu ba. Haka kuma ba wanda ya taɓa nuna baƙin cikinsa ko ɓacin ransa a lokacin da shanunsa ko tumakinsa da awakinsa ko talo-talo ko agwagi da kajin da yake kiwo suka samu yawan albarkar ’ya’ya! Sannan kuma a iya saninmu da tarihin rayuwar al’ummomin duniya, ba a taɓa samun waɗansu mahankalta da suka nuna ƙyamatar yawan haihuwar ’ya’ya a cikin jama’arsu ba!
Sai a waɗannan ’yan shekarun na ƙarshen zamani ne da gaskiyar imani da sakankancewar mutane da Allaah ta yi kaɗan, tawakkalinsu ga Mahaliccinsu Ubangijin Halittu ya yi rauni, shi ne muke jin labarin yadda waɗansu shugabanni kamar na ƙasar Sin sun gwada kafa wa mutanensu dokar hana haihuwa bayan ɗa na farko! Amma tun kafin a yi nisa sai su da kansu suka fahimci mummunar ta’asa da ɓarnar da bin wannan dokar za ta jawo musu: Na yawaitan tsofaffi da ƙarancin yara matasa, da kuma yawaitan maza da ƙarancin mata a cikinsu! Don haka, nan da nan suka janye wannan shu’umar doka, suka zauna lafiya!
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: