*185 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*YA MATSAYIN SALLAR MAI YOYON FITSARI?*
TAMBAYA:
Assalamu Alaikum, mutum yake fama da wata larura ta idan ya yi fitsari ko zai kai minti nawa ne da ninyar ya gama fitsarin amma in bayan ya sanya wandonsa sai wani dan kadan ya biyo baya, kuma ya yi magani amma bai warke ba, saboda haka in ya tashi daga fitsarin sai ya dan shafa ruwa a wandonsa sannan ya yi alola ya matsayin sallarsa?
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, Sallarsa ta yi, saboda yoyon fitsari ba ya hana yin sallah, ya ci gaba da yin yadda yake yi ɗin nan, sai dai malaman Fiqhu sun ce wanda yake yin yoyon fitsari (Tasalsulul Bauli), duk in zai yi sallah sai ya sabunta alwala, to wannan shi ne abin da ya kamata mai fama da irin wannan matsala ya kiyaye.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu zarewa*
17/11/1440 h.
20/07/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: