*ABUBUWAN DA BASA KARYA AZUMI*

528 11 0
                                    

*_MAL AMINU IBRAHIM DAURAWA_*
~°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°~
*ABUBUWAN DA BASA KARYA AZUMI*

ABUBUWA DA DAMA SUNA FARUWA GAMAI AZUMI, AMMA BASU SHAFI INGANCIN AZUMINSA BA, KAMAR YADDA DALILAI SUKA TABBATAR, GA 20 DAGA CIKI.

*NA DAYA:* CIN ABINCI DA MANTUWA

*NA BIYU:* SHAN ABIN SHA DA MANTUWA

*NA UKU:* SADUWA DA MACE DA MANTUWA

*NA HUDU:* RINJAYAR FITAR AMAI,

*NA BIYAR:* YIN ALLURA TA JIJIYA KO TA NAMA KO TA MASU CIWAN SUGAR

*NA SHIDA:*  BAYAR DA GUDUNMAWA NA JINI,

*NA BAKWAI,:* HADIYE MIYAU KO MAJINA.

*NA TAKWAS:*, JIN RAUNI KO CIWO.
*NA TARA,:* JIN KANSHIN TURARE NA RUWA, KO NA HAYAKI
*NA GOMA:*  SA KWALLI KO TOZALI A IDO.

*NA SHA DAYA:* DIGA MAGANI A KUNNE KO A IDO, BANDA HANCI.

*NA SHA BIYU:* YIN ASWAKI KO MAKILIN DA BURUSH, AMMA A KUSKURE BAKI SOSAI, KADA ZAKIN YA WUCE.

*NA SHA UKU:*, DANDANA ABINCI, AMMA KADA A HADIYE.

*NA SHA HUDU,* SHAKAR MAGANI MASU CIWAN ASMA, DOMIN HANYAR ISKA YAKE BI.

*NA SHA BIYAR:* SHAKAR KURA, KO HAYAKI, AMMA BANDA NA SIGARI

*NA SHA SHIDA:*  WANDA YAYI MAFARKI YANA AZUMI HAR YA FIDDA MANIYYI, SAI YAYI WANKA, AMMA AZUMINSA YANA NAN.

*NA SHA BAKWAI, :* WANDA YAYI JANABA DA DADDARE AMMA BAIYI WANKA BA ,SAI BAYAN ALFIJIR YA KETO.

*NA SHA TAKWAS,:* YIN WANKA DA JIKA JIKI DON SANYI

*NA SHA TARA:*  IDAN WANI KWARO KO GUDA YA SHIGE MASA BAKI, YA WUCE ZUWA CIKI BABU KOMAI

*NA ASHIRIN :* IDAN WANI YAYI MASA TILAS YA KARYA AZUMI, YA JI TSORAN RANSA YA KARYA, BABU KOMAI AZUMINSA YANA NAN.
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now