*SHIN ZA A IYA RAMA WA MARAS LAFIYAN DA YA RASU AZUMIN DA AKE BIN SA?*

294 8 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN ZA A IYA RAMA WA MARAS LAFIYAN DA YA RASU AZUMIN DA AKE BIN SA?*

TAMBAYA:

Assaalamu Alaikum Malam. Mutum ya kwanta ciwo har lokacin azumin watan Ramadan ya zo bai da lafiya kuma ga shi Allah ya yi nashi ikon ya karbi abinsa. Shin malam matarsa ko dansa za su iya ranka masa azumin sa?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, duk maras lafiyar da ya sha azumin Ramadana, bai warke ba har mutuwa ta zo masa, to ba sai an rama masa ba, babu komai a kansa, haka nan babu komai a kan iyalansa, saboda wannan uzuri na rashin lafiya. Haka nan mai shayarwa, ko mai cikin da ba sa iya ɗaukar azumi, su ma idan suka mutu kafin lokacin ramuwa, to babu komai a kansu ko a kan iyalansu na ramuwa.

Duba Majmu'u Fatáwá na Allama Ibn Baz 25/210.

Amma idan maras lafiyar ya warke kafin ya rasu, ya kuma sami ikon ramawa sai ya yi sakaci har ya rasu bai rama ba, to wannan shi ne za a rama masa, haka nan mai shayarwa da mai cikin da ba sa iya yin azumi, matuqar lokacin rama azumin ya yi, kuma sun sami dama amma suka yi sakaci ba su rama ba har mutuwa ta zo masu, to su ma duk za a rama masu azumin da ake bin su a bisa ɗaya daga cikin maganganu uku (3) da malaman Fiqhu suka yi, saboda hadisin da Manzon Allah ﷺ ya ce: "Duk wanda ya mutu akwai bashin azumi a kansa, to waliyyinsa ya yi masa".
Bukhariy 1952, Muslim 1147.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
11/7/1440 h.
18/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now