*001 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN YA HALASTA MUTUM YA SANYA KAYAN DA MACE DA NAMIJI SUNA IYA SAWA, WATO (UNISEX)?*
TAMBAYA:
Assalamu Alaikum, dan Allah tambaya nake da ita game da hadisin da ya ce Allah ya tsine ma namiji mai sa kayan mata da mace mai sa kayan maza. To wai ko kaya ne unisex kika siya kika fara sa wa ‘ya mace, to a gaba ko kin sake haihuwa sai ya kasance namiji ne ba za a sa masa ba, shin in an yi haka tsinuwa na kan uwa? Sannan ita ma mace ba za ta sa kayan mijinta ba, shin duk hukuncin haka yake?
AMSA:
Wa’alaikumus salam, wancan hadisi da Annabi s.a.w ya ke cewa: Allah ya tsine wa namiji mai sa kayan mata, da kuma matar da take sa kayan maza, tabbas haka abin yake. Sai dai abin yana buqatar tafseeli, wato rarrabewa:
1. Akwai kayan da suka keɓanci mata kaɗai, to waɗannan idan na miji ya yi amfani da su, shi ne wanda wannan tsinuwa take kansa, misali abin wuya, awarwaro, takalmin mata mai qwas-qwas, wando da riga da aka yi su don mata kaɗai, hijabi da sauransu. Duk namijin da ya sa waɗannan ya shiga cikin wannan tsinuwa.
2. Akwai kayan da aka yi su don maza kaɗai, misali wando da riga na maza, kamar kaftani ko babbar riga, ko hula, takalmi mai rufi na maza (cover shoe) da sauransu. Duk macen da ta sa waɗannan ita ma ta shiga tsinuwar Allah.
3. Akwai kayan da aka yi tarayya a tsakanin maza da mata, kamar takalmi silifas, ko zobe na azurfa, yadin qyalle da za a siya a yanka a ɗinka, da sauransu, duka waɗannan maza da mata sun yi tarayya a ciki, don haka idan mace konamiji suka sa waɗannan ba wata tsinuwa a kan ko ɗaya, saboda kaya ne na tarayya.
Amma game da kayan miji kuwa, matuqar kaya ne da suka keɓanta ga maza kawai, ba shi halasta matarsa ta sa, saboda wancan hadisin da Annabi s.a w. ya ce Allah ya tsine wa namiji mai sanya kayan mata, da mace mai sanya kayan maza.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
28/11/2018
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: