*008 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*INA AYAR DA KE MAGANA A KAN KISFEWAR WATA?*
TAMABAYA:
Assalamu alaikum malam an wuni lafiya ina da tambaya, ayar da yake magana akan kisfewar wata.
AMSA:
Wa'alaikumus salamu. Ban fahimci wace aya ce kike nufi a kan kisfewar wata ba, in kuma waɗannan ayoyin na suratul Qiyama ce kike nufi, to kuma ban fahimci me kike so a fitar a game da su ba, amma dai ga su nan:
فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ * وَخَسَفَ الْقَمَرُ * وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ * يَقُولُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ * كَلَّا لَا وَزَرَ * إِلَى رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ * يُنَبَّأُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَKuma na dai san cewa a hadisai ingantattu Annabi s.a.w ya ce:
إن الشمس والقمر آيتان من آيات الله، لا ينكسفان لموت أحد ولا لحياته، فإذا رأيتم فصلوا وادعوا الله.
MA'ANA:
Lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, ba sa kisfewa saboda mutuwar wani mutum ko rayuwarsa.
A qarshen hadisin sai Annabi s.a.w ya ce: Duk lokacin da kuka ga hakan, to ku tashi ku yi sallah, ku yi ta addu'a har a yaye maku (kisfewar).
A duba Sahihul Bukhari, babin da ke magana a kan sallar kisfewar rana, hadisi mai lamba ta 996. Wannan shi ne abin da ya tabbata daga Annabi s.a.w.
Allah ne mafi sani.
JAMILU ZAREWA.
5/4/1440 H.
12/12/2018 M.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: