*YA HUKUNCIN MARAS LAFIYAN DA BA YA IYA AZUMI?*

203 4 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN MARAS LAFIYAN DA BA YA IYA AZUMI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum.
Malam ina da tambaya, ana bi na azumi biyar to saboda na yi rashin lafiya ba na  iya rike yunwa, a hankali na fara ramawa, a na hudu da na yi sai da aka kara min ruwa, zan ci  gaba sai aka ce in huta daga baya sai na ci gaba, to gas hi kuma ba ni da lafiya shine nakeson a fada min ya zan yi? Wasu sun ce na ciyar daga baya sai na rama.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa duk rashin lafiyar da ke hana iya ɗaukar azumi da likitoci suka tabbatar da cewa ba a tsammanin warkewarsa, to azumi ya faɗi a kan wannan maras lafiya ɗin, abin da zai yi shi ne ciyar da miskini ɗaya a madadin kowane azumi ɗaya. Kuma wannan shi ne hukuncin tsoho tukuf da ba ya iya yin azumi alhali hankalinsa na tare da shi.

Amma idan rashin lafiyar  da ya hana yin azumi ana tsammanin warkewarsa, to za a jira ne idan Allah ya sa an sami waraka, sai a rama azumin da aka sha a wasu ranakun na daban, kamar yadda aya ta 185 ta cikin suratul Baqara ta bayyana.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
3/Ramadan/1440 h.
08/05/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now