*TAQAITACCEN BAYANI A KAN ZIKIRI

361 0 0
                                    

*197 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*TAQAITACCEN BAYANI A KAN ZIKIRI*

TAMBAYA:

Assalam Alaikum. lna kwana malam barka da warhaka Malam don Allah haske nake son a kara min akan Azkar da abubuwan da ake fada yayin Azkar, na gode.

AMSA:

Wa'alaikumus salam, to ita dai kalmar Azkar kalmace ta Larabci, kuma jam'i ne na kalmar Zikir, wadda ke da ma'anar ambato, ko tunawa d.s.
Amma a Musulunci idan aka ce Azkar (أذكار) ana nufin zikirori da suka qunshi karatun Alqu'ani da addu'o'i da salatin Annabi ﷺ da istigfári da kuma abin da ya jiɓanci hakan.

Mafificin zikiri shi ne karatun Alqu'ani mai girma, duk wani zikiri da mutum zai yi yana bayan karatun Alqur'ani mai girma ne. Kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya yi umurni da yin zikiri a wurare da dama a cikin Alqur'ani mai girma daga ciki sun haɗa da inda Allah yake cewa:

1- "Ya ku waɗanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". Suratul Ahzáb: 41.
2- "Ku ambace ni zan ambace ku, kuma ku gode mini kada ku kafirce min". Suratul Baqara: 152.
3- "Ku roqi gafarar Ubangijinku, sannan ku tuba zuwa gare shi". Suratu Huud: 3.
4- "Ku roqi gafarar Allah, lallai Allah mai gafara ne mai rahama" Suratul Baqara: 199.

Ku roqi gafara a nan ana nufin ku yi istigfári. Daga cikin zikirori akwai zikirin Safiya da Yammaci, da zikirin kwanciya barci da na tashi daga barci, da na shiga banɗaki da na fita, da zikirin shiga gida da na fita, da zikirin hawa ababen hawa, sannan akwai zikirorin da ake yi bayan an idar da sallar Farillah, don samun zikirorin da ake yi bayan an idar da sallar farillah sai a duba Amsoshin Tambayoyinku na 144, sai kuma a duba amsar tambaya ta 123 don samun zikirin da ake yi idan mutum ya shiga matsananciyar damuwa ko baqin ciki.

A tambaya ta 003 kuma za a sami addu'ar da Manzon Allah ﷺ kan yi wa mamaci. Sai kuma a duba tambaya ta 010 don samun addu'ar Istikhara, tambaya ta 023 za a sami addu'ar neman tsari da ake yi wa qananan yara, idan aka dubi tamabaya ta 047 kuma za a sami addu'o'in warware sihiri, idan aka duba tamabaya ta 054 za a sami addu'ar da ake karantawa idan wani ɓangare na jikin mutum yana ciwo.

Duka waɗannan a taqaice ne, ki tintuɓi ingantattun malaman Sunnah don samun zikirori ingantattu na Manzon Allah  ﷺ. Kuma ki nemi littafin GARKUWAR MUSULMI, wato (HISNUL MUSLIM), shi ma za ki fa'idantu ba ɗan kaɗan ba, saboda nan ba zai yiwu a iya kawo maki zikirorin nan yadda ya dace ba, sai dai kawai a yi taɓa ka lashe a nan.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
4/12/1440 h.
05/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now