*WACCE ADDU'A ZAN YI DON KAR IN YI BARCI BAYAN ASUBAHI

149 0 0
                                    

*198 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*WACCE ADDU'A ZAN YI DON KAR IN YI BARCI BAYAN ASUBAHI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam, ina kwana? Tambayata ita ce mutum idan ya tashi da safe ba zai iya addu'a ba akwai wata addu'a dan kar bacci ya dauke shi, kuma shin idan yai bacci ya yi laifi? Allah ya taimaka Ameen.

AMSA:

Wa'alaikumus salam, Ba wata addu'a a Sunnah da ake karantawa don ta hana mutum yin barci bayan sallar Asubahi, idan kuma akwai to ni ban san ta ba, babu laifin komai ga wanda ya yi nufin yin azkar sai barci ya ɗauke shi kafin ya kai ga wannan azkar ɗin, Allah shi ke cire ran mutane a lokacin da barci ya ɗauke su, saboda haka ba ki da laifin komai don kin yi nufin yin azkar ɗin Safiya sai barci ya ɗauke ki, ko Bahaushe ma ya ce "barci ɓarawo ne", duk lokacin da kika farka sai ki yi azkar ɗin.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
4/12/1440 h.
05/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now