*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*INA DA ULCER MAI SA YINWA DA WURI, KUMA ANA BI NA AZUMI NA SHEKARA UKU SABODA HAIHUWA DA SHAYARWA, YA ZAN YI?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, ya zan yi ramuwar azimin shekara uku da ban yi ba a dalilin haihuwa kuma ina da olsa kuma mai sa ni yinwa da wuri ce?
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, a lokacin da Allah S.W.T. ya wajabta yin azumin Ramadana a kan Muminai, sai ya kawo sauqi ga marasa lafiya da matafiya a kan shan azumin, su kuma rama a wasu ranakun na daban, da kuma ya matsa gaba sai ya ce: "Abin da ke kan waɗanda ba sa iya azumin shi ne fidiya, ciyar da miskinai..." Suratul Baqara, aya ta 183 - 184.
Malamai sun yi ma wannan aya fassarori mabambanta, amma ba za mu tsawaita bayaninsu a nan ba, kawai abin da ke kan ki shi ne kowane azumi ɗaya ki ciyar masa da miskini ɗaya a madadinsa. Kuma wannan shi ne hukuncin waɗanda suka gaza yin azumi saboda tsananin tsufa, ko rashin lafiyar da ba ta da alamar warkewa, kuma ba za ta bar su su iya yin azumi ba.
Don neman qarin bayani sai a duba Aljámi'u Li'ahkamil Qur'an 1/668-671
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
30/6/1440 h.
07/03/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Historia Corta*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: