*Tambaya ta 109*
*ƘARIN HASKE A KAN: ‘TANA TAKABA, KUMA GA LECTURES* ’
Bayan an yaɗa *Tambaya ta 005* da amsarta wanda na rubuta a ran 6/1/2018 a kan cewa, mai takaba tana iya fita zuwa ɗaukar lacca a jami’a a bisa waɗansu sharuɗɗa da na ambace su, sai jiya talata 9/7/2019 wani ya rubuta cewa: *Abin mamaki! Ta yaya za a bayar da irin wannan fatawar?!* Daga nan sai kuma ya yi dogon bayani mai soke wannan fatawar, ya ce:
1. Hadisin da aka kawo cewa ya yi, mace mai takaba tana iya fita ta je gonar dabino, don ta samo abin da ’ya’yanta za su ci.
2. Hadisin yana magana a kan abin da ya ke larura ne, wanda rashinsa zai iya kai wa mace ta rasa lafiyarta, ko kuma ta rasa rayuwarta, ko na ’ya’yanta!
3. Rashin ‘attendance in lecture’ ba zai cutar da lafiyarta, ko ya jefa rayuwarta a cikin hatsari ba.
4. In ko haka ne, wannan shi ake ce mar: *Al-Qiyaas Ma’al Faariq.* Yin hakan kuma bai halatta ba, saboda ba a tare su ke ba ta fuskar hukunci.
5. Akwai abubuwan da ya kamata a duk lokacin da za a yi Qiyaasi a dube su da idon basira, saboda hukunci ya yi daidai, su ne: (الضروريات) da (الحاجيات) da (التحسينات).
Wannan ne abin da ya faɗa a taƙaice.
*AMSA A109:*
[1] Ba abin mamaki ba ne a samu bambancin fatawa a kan mas’alolin fiqhu, saboda bambancin mahangar da malamai suke duban mas’ala. Muhimmin abu dai shi ne: Kowannensu ya ji tsoron Allaah, kuma ya gina bincikensa da maganganunsa a kan tubali ƙaƙƙarfa na ilimi, ba son-zuciya ko bin sha’awar-rai ko shaci-faɗi ba. Haka kuma ba domin hassada ko ganin-ƙyashi da sauran munanan ɗabi’u irin waɗannan ba. Abu ne sananne dai cewa: Idan malamai suka kiyaye hakan, to ba za su rasa samun lada a wurin Allaah ba, ko da kuwa sun yi kuskure ne a wurin hukuncin, balle kuma sun dace da daidai.
Babu wani malami guda a bayan Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ da ya zama tsararre daga yin kuskure, ko mantuwa, ko zamiya a cikin maganganunsa na ilimi. Don haka, dole ne duk malami na-Allaah ya zama cikin shirin karɓar gyara daga duk inda ta fito, matuƙar dai kuskurensa a cikin maganganunsa da fatawoyinsa sun bayyana.
Wannan shi ne matsayinmu, _in shaa’al Laah_ a kan duk maganganu da rubuce-rubucen da muke yaɗawa a cikin al’umma. Amma dai abu ne muhimmi a nan mu bayyana cewa: Babu wani malami guda ɗaya da muka kafe a kan cewa shi ne kaɗai muke bin ra’ayinsa da fahimtarsa, ban da sauran malamai na-da da na-yanzu. Amma muna ɗaukar dukkansu da kyakkyawan matsayi, muna bin maganganunsu, matuƙar dai mun fahimci dalilansu, kuma mun natsu da su. Sannan kuma ba sai mun maimaita ba cewa: Ra’ayoyin malaman Sunnah masana Fiqhun hadisi su muka fi gamsuwa da fifitawa a kan waɗanda ba su ba, ko malaman da ne ko na-yanzu.
[2] Maganar cewa: Hadisin da aka kawo cewa ya yi: Mace mai takaba tana iya fita ta je gonan dabino, don ta samo abin da ’ya’yanta za su ci.
A gaskiya wannan hadisin sahihi dai bai ce haka ba.
Al-Imaam Muslim a cikin As-Saheeh (1483), da Abu-Daawud a cikin As-Sunan (2297), da An-Nasaa’iy a cikin As-Sunan Al-Mujtabaa (3550) da kuma As-Sunan Al-Kubraa (5714), da Ibn Maajah a cikin As-Sunan (2034), da Ahmad a cikin Al-Musnad mai ɗauke da Takhreej na Al-Arnaa’uut (14485) suka riwaito shi, daga Jaabir Bn Abdillaah _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya ce:
An saki innata, sai ta yi nufin ta je ta yanke 'ya'yan itacen dabinonta, sai wani mutum ya hana ta. Sai ta tafi ta gaya wa Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ sai ya ce:
بَلَى فَجُدِّي نَخْلَكِ ، فَإِنَّكِ عَسَى أَنْ تَصَّدَّقِي ، أَوْ تَفْعَلِي مَعْرُوفاً
A'a! Ki je ki yanko 'ya'yan dabinonki, domin za ki iya yin sadaka, ko kuma ki yi wani aikin alkhairi.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Nouvelles*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: