*_CIN ABINCI KO SHAN WANI ABU DA MANTUWA GA MAI AZUMI_

280 4 0
                                    

*_CIN ABINCI KO SHAN WANI ABU DA MANTUWA GA MAI AZUMI_*

*Wanda ya karya azumi a bisa kuskure*

Idan mai azumi ya ci abin ci, yana mai zaton rana ta fadi,ko kuma yana zaton alfijir bai bullo ba, amma sai savanin haka ya bayyana,to babu ramuwa a kansa, saboda fadin Allah Madaukakin Sarki:
*(Babu laifi a kanku cikin abin da kuka kuskure yin sa,amma abin da zukatanku suka yi da gangan (shi ne wanda Allah yake kama ku da shi) Allah mai yawan gafara ne mai jin qai)*
@Al-ahzab;5

Hakanan saboda fadin Manzon Allah ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ )
*(Haqiqa Allah ya dauke wa al’ummata laifin kuskure,da mantuwa, da abin da aka tilasta su a kai)*
@Ibn Majah ne ya rawaito shi.

        Allah ne mafi sani

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now