*172 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN AKWAI SALLAR NAFILA MAI RAKA'O'I DA YAWA SALLAMA DAYA?*
TAMBAYA:
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته
Malam shin akwai wani hadith da yai magana kan Manzan Allah s a w ya yi sallar nafila raka'o'i da yawa amma sallama daya?
AMSA:وعليكم السلام ورحمة الله وبركاته،
Tabbas ƴar uwa akwai hadisin da Nana A'isha ta ruwaito a lokacin da aka tambaye ta game da sallar wuturin Manzon Allah ﷺ sai ta ce: Lallai Annabi ﷺ ya kasance yakan yi sallah raka'o'i tara, ba ya zama a tsakanin raka'o'in sai a raka'a ta takwas, sai ya ambaci Allah ya gode masa, sannan sai ya yunqura ba tare da ya yi sallama ba, sai kuma ya tsaya ya sallaci raka'a ta tara, sai kuma ya zauna ya ambaci Allah, ya gode masa, ya kuma yi addu'a, sannan kuma ya yi sallama har yakan jiyar da mu, sannan sai ya qara yin raka'o'i biyu bayan sallamar can da ya yi, sun zama duka raka'o'i goma sha ɗaya kenan. Sahihu Muslim 746.Wannan sai ya nuna ashe Annabi ﷺ yakan yi sallar nafila raka'o'i da yawa amma da sallama ɗaya. Amma sai dai Imam Abu Haneefa ya ce mutum ba shi da damar ya wuce raka'o'i takwas ba tare da ya yi zaman tahiya ba a sallar nafila ta dare, a sallar nafila ta yini kuwa ba zai wuce raka'o'i huɗu ba tare da ya yi zaman tahiya ba .
Duba Sahihu Fiqhus Sunna 328.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
5/11/1440 h.
08/07/2019 m.Sahihu Fiq'hus Sunnah 1/328.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: