*Tambaya ta 005:*
*TANA TAKABA, KUMA GA ‘LECTURES’*
_As Salamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh._
_Please,_ ina da tambaya: _‘Daughter-in-law’_ na tana _‘300 level’,_ yanzu ga takaba ta same ta. Shin za ta iya zuwa _‘lectures?’_
*AMSA A005:*
_W alkm slm w rhmt laah wa barakaatuh._
[1] Al-Imaam Muslim ya fitar da hadisi (Lamba: 1483) da isnadinsa sahihi har zuwa ga Sahabi Jaabir Bn Abdillaah _(Radiyal Laahu Anhumaa)_ ya ce:
An saki innata, sai ta yi nufin ta je ta yanke 'ya'yan itacen dabinonta, sai wani mutum ya hana ta.
Don haka, sai ta tafi ta gaya wa Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam),_ sai ya ce:*بَلَى فَجُدِّي نَخْلَكِ ، فَإِنَّكِ عَسَى أَنْ تَصَّدَّقِي ، أَوْ تَفْعَلِي مَعْرُوفاً*
*A'a! Ki je ki yanko 'ya'yan dabinonki, domin za ki iya yin sadaka, ko kuma ki yi wani aikin alkhairi.*Watau kamar ta yi kyauta, ko sada-zumunci, da sauransu.
[2] Dukkan Malaman Fiqhu irinsu: Maalik da At-Thawriy da Al-Laith da As-Shaafi'iy da Ahmad, ban da Abu-Haneefah sun yarda cewa: Wannan hadisin dalili ne a kan cewa mace *mai idda* tana iya fita daga gidanta da rana, idan akwai larurar da ta janyo ta ga hakan, (kamar abin da hadisin ya nuna, na zuwa yin aiki a cikin gonarta, ko wani abin da ya yi kama da hakan).
[3] Amma har Abu-Haneefah ya dace da su wurin amincewa cewa: *Mai takaba* tana iya fita, idan aka samu irin larurar da ta sanya mai idda ta fita.
Haka Al-Imaam An-Nawawiy ya kawo waɗannan maganganun a cikin sharhinsa ga wannan hadisin a cikin Sharhu Muslim.
[4] A ƙarƙashin hasken wannan hadisin da waɗannan kalamai na manyan malamai za mu iya gane cewa:
*Mai takaba* tana iya fita daga gidanta ko ɗakinta domin larurar zuwa ɗaukar lectures a jami'a, ko dai wata makaranta irinta, amma a ƙarƙashin kulawa da wasu manyan ƙa'idoji kamar haka:
1. Daga ta gama abin da ya fitar da ita, sai ta yi gaggawan komawa gida. Kar ta tsaya hira, ko yin duk wani abin da ba shikenan ba.2. Kuma lallai ta tsare dokokin da aka ɗora wa mai takaba, tun daga lokacin da ta fito daga gida har zuwa ta koma. Watau:
(i) Ba za ta sa kayan kwalliya irinsu ɗan-kunne da sarƙa da warwaro da makamantansu ba.
(ii) Ba za ta sa tozali ko gazal ko _eye-shadow_ da lalle ko _dyes_ ba, balle su jan-baki da hoda da sauransu.
(iii) Ba za ta sanya tufafi masu launi na ado, kamar leshi da shadda da sauran nau'ukan atampa masu tsada da ake yin ado ko kwalliya da su ba.
(iv) Za ta dawwama a cikin hijibinta na shari’a.
(v) Ba za ta sanya turare da sauran kayan shafe-shafe masu ƙanshi a jikinta ko a kanta ko a tufafinta ba.
3. Haka za ta zauna har sai ta yi tsawon *watanni huɗu da kwanaki goma,* daga ranar da mijinta ya rasu.
Allaah ya ƙara mana shiriya da ƙoƙarin tabbata a kan bin dokokin Al-Qur'aan da Sunnah bisa fahimtar Magabatan wannan al'umma, domin samun tsira a duniya da barzahu da lahira.
_Wal Laahu A'lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
06 - 01 - 2018
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: