SHIN WAI DA GASKE NE ANNABI S.A.W BAI YI SALLAR WALHA BA?*

171 0 0
                                    

*188 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN WAI DA GASKE NE ANNABI S.A.W BAI YI SALLAR WALHA BA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum Malam. Ina da tambaya ce a kan sallar nafila ta walha da ake yi, malam an ce annabi S.A.W. bai yi sallar walha ba, kuma ya matsayin sallar walha yake a cikin sauran nafilolin?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, ƴar uwa sallar Walha sunnah ce Mustahabbiya, kuma akwai hadisai ingantattu da dama da suka tabbatar da ingancin Sallar Walha daga Manzon Allah ﷺ, daga ciki sun haɗa da:

1. Hadisin da Abu Zarri Allah ya qara masa yarda ya ruwaito cewa: Annabi ﷺ ya ce: "A kan kowace gaɓa ta ɗayan cikinku sadaka na iya kasancewa, kowane TASBIHI sadaka ce, kowane TAHMIDI sadaka ce, kowace HAILALA sadaka ce, kowace  KABBARA sadaka ce, yin UMURNI DA ALHAIRI sadaka ce, HANI GA ABIN-QI sadaka ce, yana isarwa ga sadaka yin raka'o'i biyu na Walha" Muslim 720.

2. Abu Buraidata Allah ya qara masa yarda ya ruwaito cewa: Lallai Annabi ﷺ ya ce: "A jikin mutum akwai gaɓoɓi guda ɗari uku da sittin (360), yana iya yin sadaka da kowace gaɓa daga cikinsu", sai Sahabbai suka ce: Wanda kuma ya gaza fa ya Manzon Allah? Sai Manzon Allah ya ce: "To ya rufe majinar da ya gani a masallaci, ko ya kawar da abu mai cutarwa a kan hanya, idan bai sami iko ba sai ya yi raka'o'i biyu na Walha sun isar masa. Abu Dáwud 5242.

A dunqule wannan na nufin duk wata gaɓa daga cikin gaɓoɓun jikin mutum zai iya yin aikin sadaka da ita, haka nan ambaton zikirori irin su Subhánallah, Alhamdulillah, Allahu Akbár da makamantansu duk sadaka ce, haka nan kuma yin raka'o'i biyu na Walha duk suna matsayin sadaka ce kamar waɗancan sadakoki.

Ƴar uwa a bisa waɗannan dalilai da ke sama sai ya zama ashe Sallar Walha tabbatacciya ce daga Manzon Allah ﷺ. Cewa Annabi bai yi ba kuskure ne da rashin sani, saboda waɗannan ba su ne kaɗai ma hadisai ingantattu da suka yi magana a kan Sallar Walha ba.

Harwayau, mafi qarancin raka'o'in Sallar Walha raka'a biyu ne, mafi yawa kuma raka'a takwas kamar yadda hadisi ya tabbatar, duk bayan raka'a biyu a yi sallama. Lokacin yin ta kuwa shi ne bayan ɗagowar rana, wato lokacin da ƴaƴan raquma suke jin zafi, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta 748 ya tabbatar. Don neman qarin bayani a kan lokacin Sallar Walha a duba amsar tambaya ta 20.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
27/11/1440 h.
30/07/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now